Matar Atiku Ta Dau Kamfen Zuwa Wani Matsayi, Ta Ba Mutane Da Yawa Mamaki A Babban Jihar Arewa

Matar Atiku Ta Dau Kamfen Zuwa Wani Matsayi, Ta Ba Mutane Da Yawa Mamaki A Babban Jihar Arewa

  • Matar Atiku Abubakar ta bawa mata mata da matasa tabbacin cewa mijinta zai kare hakokinsu
  • Matar tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya ta ce mijinta na tsare-tsaren hanyar da ta fi dacewa don magance kallubalensu
  • A cewar ta, akwai bukatar matar a arewacin Najeriya su mara wa Atiku baya

Jihar Bauchi - Rukayya Atiku Abubakar, matar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, a ranar 6 ga watan Disamba, ta dira jihar Bauchi don yin kamfen gabanin babban zaben 2023.

Ta isa Bauchi don neman mata su goyi bayan mijinta tare da mambobin kungiyar ta na Princess Rukaiya Atiku Campaign Organisation (PRACO), rahoton Pulse.ng.

Rukaiya Atiku
Matar Atiku ta tafi Bauchi zuwa yi masa kamfen. Hoto: PDP, Rukaiya Atiku Abubakar.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: Baba-Ahmed Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Yan Takarar Shugaban Kasa 2 da Ba Zasu Iya Kashe Kudin da Suka Tara Ba

Ziyarar da Rukaiya ta kai jihar Bauchi na zuwa ne bayan kamfen da wasu ayyuka da ta fara tun fara yakin neman zabe.

A baya-bayan, Rukaiya ta shirya tarukan jin ra'ayin mutane a yankunan arewa da dama don tattauna hanyoyin karfafa rawar da mata za su rika takawa a dimokradiyya.

Tana kuma kan gaba wurin ilmantar da mata a karkara kan shirin farfado da kasa na Atiku da samar da mafita ga dimbin matsalolin da suka shafi cigaban mata idan an zabe shi shugaban kasa a 2023, Daily Post ta rahoto.

Kuma, a wani hira Rukaiya ta ce:

"Mijina, Atiku Abubakar, shine kadai dan takarar shugaban kasa a zaben da ke tafe a 2023 da ke goyon bayan damawa da mata da matasa a gwamnati. Don haka ne ya yi alkawarin ware $10 biliyan don karfafawa matasa da mata."

Dalilin da yasa mata da matasa ke bukatan Atiku a matsayin shugaban kasa

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kirstocin Arewa Sun Yanke Shawarar Atiku Zasu Marawa Baya - Dogara

A wani taron jin ra'ayin mutane a jihar Kaduna, matar Atiku ta ce ajandar tsohon mataimakin shugaban kasar, "My Covenant with Northwest Women" an yi shi ne don karfafawa musu goyon bayan takarar shugabancin kasarsa.

Bayan ziyarar da ta kai a yakin neman zaben, a bayyane yake cewa Rukaiya tana da himma kuma a shirye take ta tallata tsare-tsaren PDP ga dukkan mata da sauran 'yan Najeriya.

Ta kuma yi alkawarin

"Ta kuma yi alkawarin shirya mata domin shiga harkokin mulki da zarar Atiku ya karbi ragamar shugabancin Najeriya a zaben shugaban kasa mai zuwa."

2023: PDP Ta Yi Wa Atiku Alkawarin Kuri'u Miliyan 2 A Jihar Filato

Jam'iyyar PDP reshen jihar Filato ta yi wa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasarta a zaben 2023, alkawarin kuri'u miliyan biyu a zaben 2023.

Shugabannin jam'iyyar ne suka sanar da hakan yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zabe na Atiku-Mutfwang a Jos, babban birnin jihar, rahoton AIT.

Asali: Legit.ng

Online view pixel