An Daure 'Dan Tsohon Shugaban Zambia A Gidan Maza Tsawon Shekaru 12

An Daure 'Dan Tsohon Shugaban Zambia A Gidan Maza Tsawon Shekaru 12

  • Kasar Mozambique tayi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa da koma baya a tsakanin kasashen Afrika
  • An dai Zargin tsohon shugaban kasar da wadaka da dukiyar kasa da halasta kudin haram
  • Alkalin ya yanke hukuncin ne dan ya zama izina ga yan kasa da suke da irin niyyar su ta cin hanci ko rashawa

An daure dan tsohon shugaban kasar Mozambique shekaru 12 a gidan yari bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa. A wani rahoto da jaridar The Punch ta wallafa.

A ranar Laraba ne wata kotu a Mozambique ta yanke wa dan tsohon shugaban kasar Mozambique Armando Guebuza hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari.

Dan Zambia
An Daure 'Dan Tsohon Shugaban Zambia A Gidan Maza Tsawon Shekaru 12 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Hakan dai ya biyo bayan wata badakalar cin hanci da rashawa da gwamnati ta tafka kuma akai amfani dashi wajen boye kudaden.

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Indonesiya Ta Amince Da Haramta Jima'i Kafin Aure

Alkali Efigenio Baptista wanda ya samu Ndambi Guebuza da laifin almubazzaranci, halasta kudaden haram da kuma amfani da kungiyoyin masu laifuka, ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Laifukan da kuka akita sun jawowa kasa asara da kuma rasa abubuwa masu muhimman da kima".

Ba Iya Dan Shugaban Kasa Aka Daure Ba

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa tsohon shugaban tsaro da leken asiri, Gregorio Leao da shugaban sashen tattalin arziki na ma'aikatar tsaro, Antonio do Rosario, na daga cikin wanda kotun ta daure.

"Laifukan da wadannan suka aikata zai kasance a matsayin wani tabo wanda baza mu taba mantawa dashi ba," in ji Alkali Efigenio Baptista.

Wannan badakalar dai ta samo asali ne bayan da wasu kamfanoni mallakar gwamnati a kasar da ke fama da talauci suka ciyo bashin dalar Amurka biliyan 2.

Kara karanta wannan

Tsananin yunwa: Bidiyon mata 'yan Arewa na wawar shinkafa a kan tunkuya ya tada hankali

Bashin da ake ganin ba bisa ka'ida ba aka ciwoshi a shekarun 2013 da 2014, domin sayen wani jirgin ruwa na kamun kifi da kuma na sa ido.

Bayanan bashin dai sun bayyana ne a cikin shekarar 2016, inda asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da sauran masu ba da gudummawa suka bawa kasar tallafin kudi.

Wani bincike gudanar ya gano dala miliyan 500 daga cikin lamunin da aka karkatar da su wanda har zuwa yanzu dai ba a san adadin kudin ba.

Da yake zartar da hukuncin bayan mako guda yana karanta hukunce-hukuncen, alkalin ya ce badakalar ta tsananta talaucin dubban 'yan Mozambique.

An yanke wa Guebuza laifin hukuncin almubazzaranci da kudaden haram da kuma hada-hadar aikata laifuka da dai sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel