Jerin 'Yan Takarar Mataimakin Gwamna Mata da Zasu Fafata a Babban zaben 2023

Jerin 'Yan Takarar Mataimakin Gwamna Mata da Zasu Fafata a Babban zaben 2023

Gabannin babban zaben 2023, ba a bar mata a baya ba a kokarinsu na tabbatar da ganin an dama da su a siyasar jiha da harkokin gwamnati.

Basu yi kasa a gwiwa ba, suna ta kokarin ganin sun dare kujerun da yawanci maza ne ke hawansu a siyasar kasar.

An dade ana muhawara kan ba mata damar shiga harkokin siyasa da mukaman shugabanci, sai dai abun mamaki shekaru 60 bayan samun yancin kan Najeriya har yanzu ba’a taba samun mace da ta taka mukamin shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ba.

Yan takarar mataimakin gwamna
Jerin 'Yan Takarar Mataimakin Gwamna Mata da Zasu Fafata a Babban zaben 2023 Hoto: Premium Times/Daily Trust/Daily Post
Asali: UGC

Sai dai kuma, wasu yan adadi na mata sun samu damar hawa mukamin mataimakin gwamna a wasu jihohin kasar.

Ga jerin matan da suke neman takarar mataimakin gwamna

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Sanata Uba Sani: Jihar Kaduna Zata yi Kewar ‘Mai Rusau’ Bayan 2023

1. Farfesa Ngozi Odu

Farfesa Ngozi Odu ita ce yar takarar mataimakiyar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Ribas.

2. Tonto Dikeh

Jarumar Nollywood, ita ce yar takarar mataimakiyar gwamna a jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Ribas.

3. Princess Tambari Hilda Dedam

Princess Tambari Hilda Dedam ita ce yar takarar mataimakiyar gwamnan jam'iyyar Accord Party (AP) a jihar Ribas.

4. Funke Akindele

Jarumar Kannywood, Funke Akindels ita ce abokiyar takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Lagas.

5. Dr. Hadiza Balarabe

Dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Uba Sani ya sake zaban Dr. Hadiza Balarabe a matsayin abokiyar takararsa a zaben 2023.

6. Suliat Nike

Jam'iyyar African Democratic Party (ADC) a jihar Ogun itama mace ta tsayar, Suliat Nike a matsayin abokiyar dan takararta na gwamna.

7. Olaniyo Olibukola Iyabode

Har ila yau, jam'iyyar AAC mace ta tsayar, Olaniyo Olubukola Iyabode a matsayin yar takarar mataimakiyar gwamna a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

2023: Abokin Gamin Atiku, Tambuwal Da Wasu Jga-Jigan PDP Sun Lallaba Gidan Tsohon Shugaban Kasa

8. Oseni Oluronke Mishozunu

A jam'iyyar ADP reshen jihar Ogun mace aka tsayar domin takarar kujerar mataimakiyar gwamna.

9. Oyewale Modupe Olayinka

Oyewale Modupe Olayinka ita ce yar takarar kujerar mataimakiyar gwamnan jihar Ogun a jam'iyyar Accord Party.

10. Injiniya Noimot Salako-Oyedele

Mataimakiyar gwamnan jihar Ogun ita jam'iyyar APC ta sake tsayarwa domin zarcewa a kujerarta.

11. Dr Aishat Lawal-Keshinro

A bangaren jam'iyyar Labour Party, Dr Aishat Lawal-Keshinro suka tsayar a matsayin abokiyar tafiyar dan takarar gwamnanta.

12. Josephine Chundung Piyo

Dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya zabi Josephine Chundung Piyo a matsayin abokiyar takararsa.

13. Umar Rakiya

Jam’iyyar SDP reshen jihar Neja ta tsayar da Umar Rakiya a matsayin yar takarar mataimakiyar gwamnanta.

14. Farfesa Kaleptapwa Farauta

A jihar Adamawa, Farfesa Kaleptapwa Farauta, ita ce yar takarar mataimakiyar gwamna na jam’iyyar PDP.

15. Ifeoma Okoya Thomas

A jihar Abia, Ifeoma Okoya Thomas jam’iyyar African Democratic Party (ADP) ta tsayar a matsayin yar takarar mataimakiyar gwamnanta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kirstocin Arewa Sun Yanke Shawarar Atiku Zasu Marawa Baya - Dogara

16. Dr. Misis Edith Ugwuanyi

Dr. Misis Edith Ugwuanyi ita ce yar takarar mataimakiyar gwamnan jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a jihar Enugu.

17. Hauwa’u Bello

Hauwa’u Bello ce za ta tsaya a matsayin abokiyar takarar Abubakar Haruna na jam’iyyar Allied People’s Movement (APM) a zaben gwamnan jihar Sokoto.

18. Hannatu Muhtar

A bangaren jam’iyyar Action People’s Party (APP), Hannatu Muhtar ce yar takarar mataimakiyar gwamna ta jihar Sokoto.

19. Misis Emana Ambrose Amahwe

Misis Emana Ambrose Amahwe ita ce abokiyar tafiyar Sanata Farfesa Sandy Ojang Onor na jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Cross River.

20. Usani Usani

A jam’iyyar PRP, Usani Usani wanda ya kasance tsohon ministan harkokin Neja Delta ya zabi Misis Arit Bassey Nsan a matsayin abokiyar takararsa a zaben gwamnan Cross River.

21. Misis Patricia Obila

Misis Patricia Obila jam’iyyar APC ta tsayar a matsayin abokiyar tafiyar dan takararta na gwamna a jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Ku zabi mijina, ya fi Tinubu: Matar Atiku ta fadi dalilan da za su sa Yarbawa su zabi PDP

22. Misis Oshilim Ishioma Rosemary

Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Delta ta tsayar da Misis Oshilim Ishioma Rosemary, a matsayin abokiyar tafiyar dan takararta na gwamna.

23. Sanata Akon Eyakenyi

Sanata Akon Eyakenyi ce yar takarar mataimakiyar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Akwa Ibom.

24. Caroline Danjuma

Jam'iyyar African Action Congreaa (AAC) a jihar Akwa Ibom ta tsayar da jarumar fim, Caroline Danjuma a matsayin abokiyar takarar Iboro Otu a zaben gwamnan 2023.

Peter Obi na faduwa zabe za mu koma Kamaru da zama

A wani labarin, Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Lawal wanda jigo ne na APC ya ce ya rasa mai jam'iyyarsa ke jira da bata fatattake shi ba duk da ya nuna baya yin dan takararta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel