Mutane Sun Shiga Rudu Yayin da Ango Ya Tsaya Jugum Yana Kallon Amaryarsa Tana Tikar Rawa A Bidiyon Aurensu

Mutane Sun Shiga Rudu Yayin da Ango Ya Tsaya Jugum Yana Kallon Amaryarsa Tana Tikar Rawa A Bidiyon Aurensu

  • Wani ango da ya ki rausayawa a ranar aurensa ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.
  • A wani dan gajeren bidiyo da Kakulemusavuli ya wallafa a TikTok, an gano amaryar tana rawa ita kadai
  • Masu amfani da TikTok sun shiga rudani kan dalilin da yasa mutumin yak i girgijewa a ranar da ya kamata ace yana cikin farin ciki

Wani kyakkyawan ango da ya sha kunu tare da murtuke fuska a ranar bikin aurensa ya shahara a duniyar TikTok.

Wani shafi a dandalin na TikTok mai suna Kakulemusavuli ne ya wallafa bidiyon sabon angon.

Amarya da ango
Mutane Sun Shiga Rudu Yayin da Ango Ya Tsaya Jugum Yana Kallon Amaryarsa Tana Tikar Rawa A Bidiyon Aurensu Hoto: TikTok/@kakulemusavuli
Asali: UGC

Mutane na ta dasa ayar tambaya bayan ganin bidiyon mai tsawon sakan 9 wanda aka wallafa a ranar Litinin, 5 ga watan Disamba.

Ango ya kasance cikin damuwa a ranar aurensa

Yayin da amaryar ke tikar rawa cikin farin ciki, mutumin ya tsaya jugum yana kallonta. Dandazon jama’a sun kewaye su sannan sun kasance cikin farin cikin ganin ma’auratan. Abun mamaki, mutumin mai mots aba duk da sautin kida da ke tashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kasance sanye da bakin gilashin ido sannan ya murtuke fuska babu alamar fara’a kuma hakan ya sanya mutane tambayar ko dai baya son auren ne.

Zuwa yanzu ba a san dalilinsa na bata rai ba, amma dai ana ta cece-kuce kan bidiyon wanda tuni ya yadu.

Wasu mutane sun bayyana cewa watakila ba shine angon ba kuma cewa yana iya kasancewa dan gayya ne kawai.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@dianahkebong ta tambaya:

“Menene dalilin da yasa nake dariya?”

@KINGDOM ya yi martani:

“Da alama kamar kin tilasata gayen nan yin auren nan ne.”

@paduathomas317 ya ce:

“Toh. Me ya samu rigar kwat dinsa.”

Ku garzaya Facebook akwai mazan aure a chan, amarya ta shawarci yan mata

Wata kyakkyawar matashiya ta cika da farin ciki bayan ta yi gamon katar a dandalin Facebook inda ta hadu da wani hadadden gaye kuma ta yi wuff da abun ta.

Da take wallafa hotunan aurensu, budurwar ta shawarci yan mata da su dunga kula masu aike masu da sakonni don cewa akwai mazan aure burjik a dandalin na soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel