"Kar Ku Damu Da Abinda Mutane Zasu Faɗa" Kyakkyawar Budurwa Da Ta Gama Digiri Ta Bude Wankin Mota

"Kar Ku Damu Da Abinda Mutane Zasu Faɗa" Kyakkyawar Budurwa Da Ta Gama Digiri Ta Bude Wankin Mota

  • Wata matashiyar budurwa mai kamfanin wanke mota ta kayatar da mutane yayin da Bidiyonta ya watsu a soshiyaal midiya
  • An ga budurwar na aikinta cikin alfahari a wani Bidiyo da Felika Mahama ya wallafa a shafinsa, wanda ya ɗan tattauna da ita
  • Yadda ta ɗauki rayuwa duk da ta kammala digiri ya sa ta sha yabo kuma ta zama abin koyi ga matasa

Wani bidiyon kyakkyawar matashiya wacce ta buɗe wurin wankin mota ya watsu a soshiyal midiya yanzu haka, tana shan yabo.

Felika Mahama ne ya ɗauki bidiyon kuma ya wallafa a shafinsa na TikTiok bayan ya ɗan tattauna da budurwar, wacce ta gama karatun Digiri a Jami'a.

Budurwa mai wankin Mota.
"Kar Ku Damu Da Abinda Mutane Zasu Faɗa" Kyakkyawar Budurwa Da Ta Gama Digiri Ta Bude Wankin Mota Hoto: @Felika_mahama1
Asali: UGC

An ga cauɗediyar budurwar tana ci gaba da sana'arta a cikin Bidiyon tana alfahari da kuma maida hankali ba tare da jin kunya ba.

Da aka tambayeta ko bata son aikin Ofis ne, ta bayyana cewa a yanzu kam ba ta sha'awar aikin Ofis. Ta ce ta jaraba wasu ayyukan daban amma daga baya ta yanke bude wurin wankin mota.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ra'ayinta, ya fi kyau mutum ya maida hankali kan burinsa na rayuwa ko menene shi maimakon ya kasa kunne yana saurarin maganganun mutane.

Mai kamfanin wanke motocin tace ba'a iyawa mutane, a ko da yaushe kokarin mutane su sare maka guiwa idan kana kokarin cika burinka.

Mutane da dama sun ƙayatu da ganin bidiyon bayan wallafa shi a shafin sada zumunta.

Kallo bidiyon anan

Jama'a sun zuba martani a shafin

@Peddypuddles yace

"Na jinjina miki, kaɗan ake samun kyawawan mata su zaɓa wa kansu wani abu da zasu rika yi don samun rufin Asiri. Ina miki fatan Alheri Allah ya ɗaukaka ki."

@Ekua Wednesday yace:

"Ina matuƙar Alfahari dake mama."

@Matured.minds yace:

"Gaskiya wannan ta san kasuwanci, ina miƙo jinjina da girmamawa."

@Naaseitutu1 tace:

"Samun irin wannan macen yana da wahala. Kada ki ƙasa a guiwa."

A wani labarin kuma Wata matar aure ta yi kicibus da Mijinta yana rage zafi da wata yar magajiya, ta zazzage musu buhun masifa a bidiyo

Babban abun da ya ƙara ɗaga wa matar hankali kuma ya ba ta mamaki shi ne yadda mijinta ya koma yana koƙarin kare yarinyar da suke tare.

Mutane sun maida martani kan halin mijin kana wasu sun bayyana yadda cin amana a zamantakewar aure ya zama ruwan dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel