Matashi Ya Girgiza Intanet Yayin da Ya Nuna Yadda Ya Makala Ma Kansa Gashin Kanti Ya Zama Gemu

Matashi Ya Girgiza Intanet Yayin da Ya Nuna Yadda Ya Makala Ma Kansa Gashin Kanti Ya Zama Gemu

  • Wani bidiyon Tiktok da ke nuna yadda wani mutum ya makala ma kansa gemu ya jawo cece-kuce a shafin yanar gizo
  • A bidiyon da aka yada, an ga lokacin da mutumin ke manna gashin kanti a habarsa, kafin daga baya ya saisaye ya zama daidai kamar gemu
  • Bidiyon ya yadu a intanet, inda ya jawo cece-kuce da martani mai daukar hankali tsakanin maza da mata

Yanzu dai ya fara zama al’adar maza rungumar kare-kare a fannin kwalliya, sabanin yadda aka san mata da yin hakan a baya.

Ba sabon abu bane a yanzu a ga namiji gandar-gandar yana karin gashi ko kuma karin farce ko ma dai manna wani abu a sassan jikinsa.

Wani bidiyon matashi namiji na manna gashin kanti da sunan dasa gemu ya jawo cece-kuce a shafin sada zumunta, ganin yadda matashin ya yi nasarar makala ma kansa gemu mai kyau.

Wani mai amfani da kafar TikTok, @dieg.13 ne ya yada bidiyon na lokacin da mutumin ke amfani da gashin kanti da wani nauyin gam da ya bashi damar cimma burinsa.

Matashi ya manna ma kansa gemu a cikin wani bidiyo
Matashi Ya Girgiza Intanet Yayin da Ya Nuna Yadda Ya Makala Ma Kansa Gashin Kanti Ya Zama Gemu | Hoto: @deig.13 (Tiktok)
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An ga daga baya lokacin da matashin ya yi amfani da almakashi wajen saisaye gashin da ya manna, sai ga gemu ya fito kamar na gaske.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a kafar TikTok

Yayin da wasu mutane suka bayyana kaduwarsu da ganin abin da matashin ya yi, wasu kuwa sun shiga mamaki. Ga dai kadan daga martanin jama’a a TikTok:

ebby.jama:

"Ya yi kyau kamar dai na gaske.”

atarhe:

"Meye bambancin tsakanin wannan da kuma yin kwalliya? Lol.”

mz_ngee:

"Kar naji wata mace a nan ta ce pim!!”

nuel_la_nigzx:

"Mata ne nake ganin sun kadu da wannan...Ku da kuke saka komai na kanti kullum.”

_stil_young:

"Ku kadai aka ce kun iya cin kasuwa da kwalliya da gashin kanti, yanzu lokacinmu ne mu ma.”

yinxybelle:

"Daidai yake da karin gashi ko kuma saka gashin kanti.”

kiskacsa:

"Ki kai shi ninkaya a ranar haduwarku ta farko.”

ButhaayHavinAsthma:

"Abin ya fi kama da shinfidar daki.”

MmathaboNgwatladiPul:

"Matsin yanzu kam ya fara yawa.”

Tela ta burge amarya, ta saka mata albarka

A wani labarin kuma, wata tela ta sanya amarya kukan dadi yayin da ta cika mata alkawarin dinka mata kayan biki.

Wani bidiyo ya nuna lokacin da amaryar ke sharbar kuka tana yiwa telar tofin albarka a bainar jama'a.

Jama'a da dama sun yi martani mai daukar hankali game da wannan bidiyon bidiyo na amaryar da ta shiga mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel