IGP Ya Tura Jami’an Tsaro Yayin da Aka Koma Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna Zai Koma Bakin Aiki

IGP Ya Tura Jami’an Tsaro Yayin da Aka Koma Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna Zai Koma Bakin Aiki

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta tura jami’an tsaro domin dakile faruwar hare-hare a titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
  • Gwamnatin Najeriya ta ce za a ci gaba da zirga-zirgar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 5 ga watan Disamba
  • An kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, wannan yasa gwamnati ta dakatar da jigilar jirgi a Tsakani garuruwan biyu

FCT, Abuja - Usman Alkali Baba, sufeto janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya ya umarci a tura jami’an tsaro domin dakile abin da ka iya faruwa a titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

IGP ya ba da wannan umarnin ne a daidai lokacin da hukumomin kasar nan ke shirin sake bude titin tare da ci gaba da daukar fasinjoji domin jigila a yankin.

Kara karanta wannan

Dakarun Soji Sun Halaka ‘Yan Bindiga 20 a Niger, Sun Yi Nasarar Ceto Wasu Mutum 5

Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Lahadi ya bayana cewa, za a zagulo jami’an ne daga ‘yan sandan mobal, K-9, jami’an leken asiri da na sashen kunce bam da kuma na sashen jirgin kasa.

An tura jami'an tsaro tashar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
IGP Ya Tura Jami’an Tsaro Yayin da Aka Koma Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna Zai Koma Bakin Aiki | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

TheCable ta ruwaito cewa, gwamanti ta amince a sake bude hanyar titin jirgin kasan Kaduna, kuma za a ci gaba da jigilar mutane daga ranar 5 ga watan Disamba, yau kenan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tattuna tsakanin hukumar ‘yan sanda da hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC)

Adejobi ya bayyana cewa, hukumar ‘yan sanda ta jima tana tattauna lamarin bude hanyar da hukumar jiragen kasan Najeriya (NRC) da ma sauran hukumomin tsaron da ke alaka da shi.

Channels Tv ta naqalto shi yana cewa:

“Tura jami’an zai game manyan tashoshin jiragen kasa da kuma hanyoyin da ake aiki akansu don ba da cikakken tsaro ga fasinjoji, dukiyoyi da ma dukkan aikin jirgin kasa domin kare aukuwar wani mummunan yanayin da ba a fata.”

Kara karanta wannan

Rikici: Makiyaya da manoma sun yi fada, an kashe mutum 8 har da yada, an kone gidaje 47 a jihar Arewa

Ya kuma ambato IPG na cewa, hukumar na yin iyakar kokarinta don tabbatar da aminci da tsaro a titunan jiragen kasa a yankin da ma sauran yankunan kasar nan baki daya.

‘Yan ta’adda sun kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

Idan baku manta ba, a baya wasu tsagerun ‘yan bindiga sun farmaki jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, inda suka hallaka mutane da yawa.

An sace mutane da yawa, wannan yasa ‘yan Najeriya ke ta cece-kuce kan yadda aka wulakanta fasinjojin jirgin.

Bayan haka ne gwamnati ta dakatar da jirgin tare da bayyana aikin ceto wadanda aka sace da kuma gano mafita ga tsaron hanyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel