Da duminsa: Yan bindiga sun tada Bam kan jirgin kasan Abuja-Kaduna mai dauke da fasinjoji 900

Da duminsa: Yan bindiga sun tada Bam kan jirgin kasan Abuja-Kaduna mai dauke da fasinjoji 900

  • Bayan hare-haren da aka kai a baya, yan bindiga sun tada Bam layin dogon titin jirgin Abuja zuwa Kaduna
  • Akalla mutum 900 jirgin ke dauka a zubi guda kuma ana zargin an kashe wasu cikin fasinjojin
  • Yan bindigan sun budewa jirgin wuta bayan tsayar da shi inda suka harbe mutane da dama ba gaira ba dalili

Jihar Kaduna - Wasu tsagerun yan bindiga da ake zargin yan ta'adda ne sun tada Bam kan layin dogon jirgin kasan Abuja-Kaduna dauke da daruruwan fasinjoji.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa wannan hari ya auku ne da daren Litnin, tsakanin garin Katari da Rijana.

Daya daga cikin fasinjojin ya bayyana cewa yan bindigan sun zagaye jirgin kuma suka fara bude wuta.

Da duminsa: Yan bindiga sun tada Bam kan layin dogon jirgin kasa Abuja-Kaduna dauke da fasinjoji 900
Da duminsa: Yan bindiga sun tada Bam kan layin dogon jirgin kasa Abuja-Kaduna dauke da fasinjoji 900
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A riwayar Daily Trust, jirgin ya sauka daga kan layin dogon sakamakon harin.

Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa:

“Babu sabis na waya a wajen saboda haka bamu san abinda ya faru ba sai jami’an da muka tura sun dawo.”
“Abun da muka sani shine an dasa bama-bamai kan layin dogo kuma jirgin ya fadi. Bamu sani ko wasu sun ji rauni ko mutuwa ba.”

A wata riwayar kuwa, ChannelsTV ta ce yan bindiga sun afka cikin jirgin kuma sun yi awon gaba da dimbin fasinjoji.

Wani fasinja, Anas Iro Danmusa, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa Bam ta lalata layin dogon kuma yan bindigan na kokarin kustawa cikin jirgin.

Layin dogon Kaduna-Kano: Da yiwuwan mu gaza kammalawa saboda rashin kudi, Amaechi

Ministan Sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya yi gargadin cewa rashin kudi na iya zama cikas ga kammala ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano.

Ministan ya bayyana cewa yanzu haka Gwamnatin tarayya na neman kudi daga wurare daban-daban don kammala aikin.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Kano yayin ziyarar ganin ido da ya kai

A baya, Ministan Sufurin ya bayyana cewa nan da karshen 2022 za'a fara amfani da layin dogon Kano zuwa Kaduna.

Amaechi ya kara da cewa Gwamnatin tarayya kawo yanzu ta zuba $400million wannan aiki kuma za'a kammala a kaddamar kafin wa'adin Shugaba Buhari ya kare a ofis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel