Wadanda Suka Sace Basaraken Ondo Sun Nemi A Biya Miliyan N100 Kudin Fansa

Wadanda Suka Sace Basaraken Ondo Sun Nemi A Biya Miliyan N100 Kudin Fansa

  • Awanni da dama bayan sace shi, yan bindigar da suka yi awon gaba da wani basarake a jihar Ondo sun tuntubi yan uwansa
  • Yan bindigar da suka sace Oloso na Oso-Ajowa Akoko, Oba Clement Olukotun, sun nemi a biya naira miliyan 100 domin su sako shi
  • Dangin basaraken na kasar Yarbawa sun koka cewa basu da wannan makudan kudade kuma basu da dalilinsu

Ondo - Masu garkuwa da mutanen da suka sace Oloso na Oso-Ajowa Akoko, Oba Clement Olukotun, sun bukaci a biya naira miliyan 100 kafin su saki basaraken.

Wani dan uwan basaraken wanda ya zanta da jaridar Thisday a sirrince ne ya bayyana yawan kudin da suka bukata, yana mai cewa masu garkuwa da mutanen sun kira da misalin karfe 6:00 na safiyar asabar, 3 ga watan Disamba don gabatar da bukatarsu.

Kara karanta wannan

Hukumar Sojojin Kasa Tace Zata Canja Fasalin Kai Hare-Hare A Fadin Nigeria

Jihar Ondo
Wadanda Suka Sace Basaraken Ondo Sun Nemi A Biya Miliyan N100 Kudin Fansa Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Yan bindigar sun farmaki gidan basaraken a Oso-Ajowa Akoko. Don samun shiga gidan kai tsaye, maharan sun yi harbi sannan suka lalata kofar shiga kafin suka dungi jan basaraken a kasa tare da yin awon gaba da shi.

A taimake mu bamu da kudaden da suka bukata, yan uwan basaraken

Majiyar ta bayyana cewa maharan sun kira daya daga cikin yan uwan basaraken sa'o'i 32 bayan ana ta jiransu sannan suka gabatar da bukatarsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan uwan basaraken ya roki gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu da yan Najeriya da su taimaka wajen kubutar da basaraken daga hannun wadanda suka sace shi, don hana yan bindigar daukar mummunan mataki.

Majiyar ta kara da cewar rundunar hadin gwiwa da ta hada da yan sanda da maharba sun fara kakkabe dazuzzuka daga Ajowa zuwa iyakokin Kogi don tabbatar da ganin cewa sun ceto basaraken, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

"Ba Bayan Gida, Babu Girki": Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

Ya ce:

"Mun samu kira daga wajensu a safiyar yau. Daya daga cikin ahlinmu ya amsa kiran waya. A yanzu za mu iya tabbatar da cewar wadanda suka kawo harin masu garkuwa da mutane ne.
"Sun bukaci a biya naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa domin sako basaraken. A ina za mu iya samun wannan makudan kudade? Wannan ya fi karfinmu.
"Muna rokon gwamnatin jihar Ondo, shugabannin karamar hukumar Akoko ta arewa maso yamma da sauran yan Najeriya da su taimaka su kawo mana agaji, don a sako Kabiyesi cikin koshin lafiya daga inda aka tsare shi."

Yan bindiga sun farmaki Sanatan jihar Neja

A wani labarin, mun ji cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kai wa Sanata Muhammad Sani Musa farmaki a gidansa da ke unguwar Tunga a jihar Neja.

Maharan sun je ne da niyar kashe sanatan mai wakiltan Neja ta gabas a majalisar dattawa amma sai ya tsallake rijiya da baya.

Kara karanta wannan

An Kama ‘Yan Najeriya da Suka Makale a Kasan Jirgin Ruwa Tsawon Kwana 11 Zuwa Kasar Spain

Asali: Legit.ng

Online view pixel