Yadda iPhone 7 Ta Jawo Jami’an Tsaro Suka Kamo Wanda Ya Ci Mutuncin Aisha Buhari

Yadda iPhone 7 Ta Jawo Jami’an Tsaro Suka Kamo Wanda Ya Ci Mutuncin Aisha Buhari

  • Festus Jossiah shi ne babban jami’in ‘yan sandan da ya jagoranci aikin cafko Aminu Adamu daga Jigawa
  • Usman Shugaba wanda shi ne babban Dogarin Aisha Buhari, ya nemi Jossiah ya bi masa sahun matashin
  • Jami’an ‘Yan Sanda sun yi amfani da wayar wannan yaro, suka tare a garin Dutse, har sai da suka kama shi

Abuja - Bayanai sun fito a game da yadda jami’an tsaro suka kamo Aminu Adamu mai karatu a jami’ar tarayya a garin Dutse, suka wuce da shi Abuja.

Premium Times tace wani jami’in rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawa, Festus Josiah shi ne ya taimaka wajen bin sawun Aminu Adamu a jihar Jigawa.

Festus Josiah yana aiki ne da rundunar ‘Anti Vice Section A’ ta shiyyar Mararaba a jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Aminu Adamu: Uwargida Aisha Buhari da Mutum 4 Za Su Bada Shaida a Kotu

A bayanin da ya gabatar, ‘dan sandan yace Dogarin Aisha Buhari watau Usman Shugaba ne ya tuntube shi bayan ganin maganar Aminu a shafin Twitter.

Josiah yana kuma aiki a ofishin Uwargidar shugaban Najeriya a matsayin jami’in da yake bibiyar salula, kuma shi ya yi sanadiyyar gano inda matashin yake.

‘Dan sandan yace shi da ‘yan tawagarsa sun kama hanya zuwa garin Dutse a jihar Jigawa a wata Litinin, suka dauki tsawon lokaci suna bibiyar wannan yaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aisha Buhari
Aisha Buhari da ADC, Usman Shugaba Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Aminu ya shiga hannu

Bayan kwanaki uku ana neman shi, sai ‘yan sandan Najeriya suka yi dace, suka cafke shi.

Jami’in yake cewa sun yi amfani da wayar shi, Iphone 7, kuma bayan an gano shi sai aka duba shafinsa na Twitter, aka tabbatar da wannan maganar da ya yi.

An karbe wayar Aminu

A halin yanzu wayar Aminu Adamu tana hannun sashen binciken ta’addanci da ke karkashin FIB a Abuja, jami’an ‘yan sanda suna bincike na musamman.

Kara karanta wannan

Jami'anj Tsaro Sun ki Su Bayyana Ko A Wanne Hali Aminu Yake Ciki Baya Da Ya Shafe Mako Guda A Hannunsu

Haka zalika, rahoton ya nuna za ayi amfani da wayar salulan wajen bada shaida idan ta kama. Shi kuma matashin sai aka wuce da shi bangaren SCID a Abuja.

Bayanan da Lauyan ‘yan sanda, James Idachaba ya gabatarwa kotu a takarda, sun hada da maganar Aminu Adamu da wayarsa ta iPhone 7 a matsayin hujja.

An tanadi shaidu a kotu

Rahoto ya zo cewa matashin dalibin da ake shari’a da shi a kotu, Aminu Adamu zai fuskanci kalubale, Matar Shugaban kasa za ta bada shaida da kan ta.

Uwargidar Najeriya da wasu 'Yan Sanda za su zama masu shaida a kotun a wannan kara, a yayin da al’umma suke rokon ayi wa yaron afuwar laifinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel