Jami'an Tsaron Nigeria Sunyi Kunnen Uwar Shegu da Batun Aminu

Jami'an Tsaron Nigeria Sunyi Kunnen Uwar Shegu da Batun Aminu

  • Aminu dai Wani Dalibi Ne dake Ajin Karshe A Jami'ar Tarayya dake Dutsen Jihar Jigawa
  • Batun Aminu Ya dau Hankalin mutane a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin bai dace da abinda yayi b, wasu kuma naganin ba abinda yayi
  • Tun Makon Ya da wuce dai aka nemi aminu aka rasa sai daga baya kuma aka samu labarinsa

Abuja: Har yanzu jami'an tsaro sunyi gum da bakin su kan wani dalibi dake Jami’ar Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, Aminu Adamu da ake zargi da sukar uwargidan shugaban Buhari a shafin Twitter.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar tsaron kasar da kuma wasu jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya ne suka dauke dalibin suka tafi da shi Abuja.

Aminu Aisha
Jami'an Tsaron Nigeria Sunyi Kunnen Uwar Shegu da Batun Aminu Hoto: The Punch
Asali: UGC

An ce wanda aka tsare din ya yi magana da wani dan uwansa a waya, inda ya ce ana tsare da shi ne bisa umarninUwar Gida Aisha. kamar yadda jaridar The Punch Ta Rawaito

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Umurnin Kai Shi Kurkuku: Shugaban Yan Sanda Nigeria Yayi Martani

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai Jami'an Tsaro Suka Ce

Kokarin jin ta bakin kakakin hukumar DSS, Peter Afunnaya, ya ci tura, domin har yanzu bai amsa kira da sakonnin da aka aika a wayarsa ba har zuwa lokacin Jardiadr The Punch ke hada wannan rahoto.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu, ya ce,

“Muna da dabarun gudanar da kama mutane a wajenmu. A ce ina Jigawa ina binciken wani lamari a Legas ko Fatakwal. ai bazai yiwuba
Idan Ina da wani abu to zan sanar da CP dina, wato maigidana, cewa ina da wata kara a Legas, sai in rubuta wa CP da ke Legas don ba ni damar kama wani da ake zargi a jihar.”

Da aka tambaye shi ko an rubuta irin wannan wasika ga kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Shiishu ya ce bai sani ba.

Kara karanta wannan

An Samu Matsala Wajen Gwajin Maganin Bindiga, An Kashe wanda Yaje Neman Maganinta

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Muyiwa Adejobi, ya ci tura, domin har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai dawo da kiraye-kirayen da sakonnin da aka aika masa ba in ji Wakilin The Punch.

A halin da ake ciki, lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya ce wadanda ke tsare da Aminu suna aikata laifi ne saboda ana tauye wa dalibin hakkin lauya.

“Dole ne su san inda yake domin lauya ya je wurin. Abin da doka ta ce. Dole ne su tuntubi dangi. Dole ne 'yan uwa su san inda yake, don su sami lauyan da zai nemi belinsa. Laifin da ya aikata kuma dole ne ace an bayyana shi,” in ji shi.

Lokacin da yake sa baki a saki Aminu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

Kara karanta wannan

Ki hakuri mama: Daliban Najeriya sun durkusa, suna nema wanda ya zagi Aisha Buhari afuwa

“Abu ne da ba a taba mantawa da shi ba kuma ba a taba ganin irinsa ba ace uwargidan shugaban kasa @Aisha Buhari ta azabtar tare da cin zarafin Aminu, har ma garin haka ya karye a kafarsa sakamakon haka. . Dole ne talaka ya sami yanci. @PoliceNG dole ne a saki #FreeAminu tare da biyansa diyya."

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Arewacin Najeriya, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakatarenta, A.A. Hikima, ya yi kira ga

Dukkan mutane da hukumomin da ke da hannu wajen kamawa da tsare Aminu ba bisa ka’ida ba da su gaggauta sakinsa tare da ba shi hakuri da kuma biyansa diyya.”

Shugaban kungiyar daliban Najeriya Usman Barambu ya nemi afuwar Aisha tare da yin kira da a sako wanda aka tsare din.

"A matsayinmu na shugabanni da masu rike da mukaman shugabanci, dole ne mu yi watsi da sukar da ake yi mana idan muna son yin gaba da yin abin da ya dace," in ji Barambu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel