An Gano Gawarwakin Mata 2 Daga Sansanin Yan Bindiga A Kaduna

An Gano Gawarwakin Mata 2 Daga Sansanin Yan Bindiga A Kaduna

  • Jaruman dakarun tsaro a jihar Kaduna na Operation Sanity sun kai samame a sansanin yan bindiga a dajin Chikun
  • Sojojin sun gano gawarwakin wasu mata guda biyu, sannan sun ceto wasu maza guda biyu daga bisani aka sada su da iyalansu
  • Mr Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna ya ce sojojin za su cigaba da fadada sintirinsu a wasu dazukan

Kaduna - Jami'an tsaron na Operation Sanity sun gano gawarwakin wasu mata biyu da ba a san ko su wanene ba da yan bindiga suka kashe kuma sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a dajin Chikun a jihar Kaduna.

Dakarun sun lalata sansani da yawa na yan bindigan a cewa kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Mr Samuel Aruwan, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Ba Bayan Gida, Babu Girki": Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

Yan Bindiga
An Gano Gawarwakin Mata 2 Daga Sansanin Yan Bindiga A Kaduna. Hoto: @daily_trust/@Bulamacartoons
Asali: Twitter

Abubuwan da sojoji su ka gano a sansanin yan bindiga a Kaduna - Aruwan

Aruwan ya ce sakon da gwamnatin Kaduna ta samu ya nuna dakarun sojojin sun fafata da yan bindigan ne kusa da Kwanti a karamar hukumar Chikun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"A yayin da yan bindigan suka tsere cikin daji, sun bar baburansu da sojoji suka dakko. Sojojin sun kona dukkan sansanin da suka gani. Da suke bincika sansanin, sojojin sun gano maza biyu da aka yi garkuwa da su, wani Muntaka Abubakar da Nwabueze John. An ceto wani Tabawa Laraba dan shekara 85 a Kuzo.
"Sojojin sun kuma gano gawarwakin wasu mata biyu da yan bindigan suka kashe."

Ya ce an kwashe gawarwakin yayin da wadanda aka ceto kuma an sada su da iyalansu, bayan basu taimako na farko, Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jami'anj Tsaro Sun ki Su Bayyana Ko A Wanne Hali Aminu Yake Ciki Baya Da Ya Shafe Mako Guda A Hannunsu

Ya ce sojojin sun fadada sintiri zuwa yankin Abrom, Gabachuwa da kuma dajin Kujeni da suka hada da kananan hukumomin Kajuru, Chikun da Kachia.

Ya ce yan bindigan sun tsere bayan hango sojojin suna tahowa sansaninsu.

Sojoji sun kashe yan ta'adda a hanyar Zaria zuwa Kaduna

A wani rahoton daban, sojojin Najeriya sun halaka wasu yan fashin daji a hanyar Zaria zuwa Kaduna a karamar hukumar Igabi.

Jami'an tsaron sun kai wannan samamen ne bayan samun bayanan sirri game da ayyukan bata garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel