Kamfanonin Waje na Iya Karbe Jiragen Fadar Shugaban Kasa a Dalilin Taurin Biyan Bashi

Kamfanonin Waje na Iya Karbe Jiragen Fadar Shugaban Kasa a Dalilin Taurin Biyan Bashi

  • Fadar Shugaban kasan Najeriya ta tara dinbin jiragen sama da kula da su yake neman zama mata wahala
  • Air Vice Marshal Abubakar Abdullahi ya fadawa majalisa ana fama da karancin kudin gyaran jiragen kasar
  • Abin da hakan zai iya jawowa shi ne a hana jiragen kasar tashi, ko kamfanonin kasar waje su yi gaba da su

Abuja - A wani rahoto daga Punch, an fahimci jiragen da ke fadar shugaban kasa suna fuskantar barazana domin kamfanonin ketare na iya karbe su.

Kamfanonin kasashen waje da ke bada bashi suna bin bashin kudi a dalilin gyare-gyare da suka yi wa jirage 10 da fadar shugaban kasa ke amfani da su.

Da wadannan jirage shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, da kuma iyalansu da manyan jami’an gwamnati ke yin tafiya a gida da wajen Najeriya.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Damke Dalibai 5 Kan Zargin Halaka Abokin Karatunsu a Sokoto

Akwai wasu ‘yan kwaskwarima da gyaran inji da ake yi wa duk wani jirign sama lokaci bayan lokaci domin a iya ba su damar tashi a sararin samaniya.

Babu isasshen kudi

Ana bukatar wasu na’urori da ya kamata a sa wa jiragen, amma jaridar Punch tace a dalilin rashin kudi an hakura da wannan maganar sai zuwa 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jami’in sojan da ke kula da jiragen saman, Air Vice Marshal Abubakar Abdullahi ya fadawa ‘yan majalisa yadda suke fama da karancin kudin yin aiki.

Duk da kasafin kudinsu ya tashi da 121% a shekaru takwas, a cikin N4.5bn da ake bukata domin kula da jiragen, AVM Abdullahi yace N1.5bn aka samu.

Jirgin Fadar Shugaban Kasa
Iyalin Muhammadu Buhari a jirgi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bayanin da sojan ya yi wa kwamitin tsaro na majalisar tarayya ya nuna kowane jirgi yana bukatar tsakanin $1.5m zuwa $4.5m domin a iya kula da shi.

Kara karanta wannan

Bayan Sauyin Launi, Buhari Ya Nuna Inda Sababbin Kudin da Aka Yi Suka Bambanta

AVM Abdullahi ya fadawa kwamitin cewa a tsawon shekaru biyar, ba a fitar da kudin da suka dace ba, saboda haka aiki da jiragen ya yi matukar wahala.

A cewarsa, bashin da kamfanoni musamman na kasar waje su ke bin jiragen saman ya taru sosai idan har aka yi la’akari da yadda Dala ta tashi a yanzu.

Sojan yace yanzu an gagara gyara jiragen Falcon 7X wanda hakan yana iya jawo a karbe jiragen a filin tashin jirage a kasashen waje ko a wajen gyara.

Baya ga haka akwai kudin inshora da ya kamata a biya kwanan nan, Abdullahi yace za ta iya kai wa jihohin gida su fara hana jiragen sauka a cikinsu.

Jiragen fadar shugaban kasa

Jiragen da fadar ta ke amfani da su sun hada da Boeing Business Jet (Boeing 737-800 ko NAF 001), Gulfstream G550, da Gulfstream V (Gulfstream 500).

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Yana Zugo Gwamnoni 36 Su Taya shi Yaki da Gwamnatin Najeriya kan Haraji

Akwai jiragen Falcons 7X biyu, Hawker Siddeley 4000, jirage biyu masu saukar ungulu kirar Agusta Westland AW139 da AgustaWestland AW101.

Kuna da labari daga baya Janar Babagana Monguno (retd) ya dauki wasu jirage masu saukar ungulu ya mallakawa sojojin sama domin a rage kashe kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel