Sokoto: Bayanai Sun fito Kan Yadda Daliban Kwaleji Suka Halaka Abokin Karatunsu

Sokoto: Bayanai Sun fito Kan Yadda Daliban Kwaleji Suka Halaka Abokin Karatunsu

  • Wasu daliban kwalejin kiwon lafiya ta Sultan Abdurrahman dake Gwadabawa a jihar Sokoto sun halaka ‘dan uwanmu dalibi kan zarginsa da satar waya
  • Daliban biyar a halin yanzu suna hannun ‘yan sanda sakamakon daure Malami da suka yi da igiya suka dinga dukansa har ya kai ga rasa ransa
  • Sun kwashi gawarsa inda suka kai ta asibiti daga bisani suka wuce gidan iyayensa tare da cewa sun gan shi cikin jini ne, lamarin da yasa ‘yan sanda suka kama shi

Sokoto - Bayanai sun fito kan yadda wasu dalibai biyar na kwalejin Sultan Abdurrahman dake Gwadabawa a jihar Sokoto suka hada kai wurin halaka wani dalibin kwalejin mai suna Lukman Malami kan zarginsa da satar waya.

Dalibin kwaleji da aka halaka
Sokoto: Bayanai Sun fito Kan Yadda Daliban Kwaleji Suka Halaka Abokin Karatunsu. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Malami, daliban dake karantar fannin hakora a kwalejin, an zargi wasu abokansa da kashe shi a safiyar Lahadi bayan sun kasa nasarar saka shi ya dawo da wayar da aka yi ikirarin ya sata.

Kara karanta wannan

Hotuna Daga Shagalin Bikin Jarumar Kannywood, Halima Atete, Jama'a Sun Yi Martani

Daliban da ake zargin sun hada da Abubakar Tukur, Ashiru Sanusi, Bashar Gada, Yakubu Awwal da Ibrahim Hussaini. Akwai Mubarak Lawal da Ahmad Abdul wadanda ba daliban makarantar bane amma ana zargin su da zama cikin wadanda suka kona Malami.

A yayin tabbatar da mutuwarsa ga Premium Times a wayar salula, Nafiu Bello, jami’in kula da harkokin dalibai na kwalejin, yace wadanda ake zargin sun daure Malami da igiya a dakinsa dake wajen makaranta inda suka yi masa duka har ya mutu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace daliban sun taru a daki daya domin murnar fitar da sakamakon jarabawarsu da aka yi.

“A yayin murnar sakin sakamakon jarabawar ne waya ta bata kuma Lukman Malami yana daga cikin daliban da suka fita daga dakin a lokacin da ake neman wayar aka rasa. A yayin da ya dawo, sun ce shi ya sace wayar kuma ya fita boyeta amma ya jaddada cewa ba shi bane.”

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matashi Ya Tashi Kan Yan Jami'a a Najeriya Bayan Ya Shiga Makaranta Da Motar Miliyan 24, Kallo Ya Koma Kansa

- Bello yace.

Yace daga bisani daliban sun daure Malami inda suka dinga dukansa da bulalai har sai da ya fita hayyacinsa.

“Sun kwasheshi zuwa asibiti lokacin da suka gane baya hayyacinsa amma ya rasu kafin su kai asibitin.”

- Yace.

Bello yace daliban daga bisani sun dauke gawarsa daga asibiti amma daga baya ‘yan sanda sun kama shi.

“A ranar Laraba, na kai wasikar korarsu ga ‘yan sanda saboda ba zamu iya cigaba da zama dasu cikin dalibanmu ba. Shugaban makarantar yayi kira ga malamai dasu jajantawa iyayen da iyalan daliban.”

- Yace.

Dakin dalibin dake wajen makaranta

Sahara Reporters ta rahoto cewa, Sanusi Malami, yayan dalibin da aka halaka, yace wadanda ake zargi da kashe shi ne suka dawo da gawarsa gida a safiyar Lahadi.

Yace daliban sun sanar da ‘yan uwansa cewa sun tarar dashi a dakinsa cikin jini yayin da suka shiga wurinsa da sassafe.

Kara karanta wannan

Mutum 23 Sun Yanke jiki sun Fadi Yayin Tattakin Goyon Baya ga Tinubu da Shettima a Kano

“Mun dauka gawar zuwa asibiti a Sokoto domin a duba abinda ya kashe shi amma sun ce sai an saka ‘yan sanda. Yayin da ‘yan sanda suka zo, sun fara tuhumar daliban sannan daga baya suka yi awon gaba dasu.”

- Yace.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, Sanusi Abubakar bai amsa kira da sakon kar ta kwana da aka tura masa ba.

Dalibai sun halaka daliba kan zargin batanci ga Annabi

A wani labari na daban, daliban kwalejin ilimi na Shehu Shagari dake Sokoto sun kone wata daliba Kirista.

Sun zargeta da yin batanci ga Annabi a wata guruf ta WhatsAp.

Asali: Legit.ng

Online view pixel