Dalilin Da Ya Sa NCAA Ta Tsare Jirgin Kamfen Din Peter Obi - Majiya

Dalilin Da Ya Sa NCAA Ta Tsare Jirgin Kamfen Din Peter Obi - Majiya

  • Hukumar kula da sufirin jiragen saman Najeriya, NCAA, ta tsare jirgin kamfen din dan takarar Peter Obi na jam'iyyar LP
  • Majiyoyi sun bayyana cewa jirgin na Peter Obi ya saba doka ne a filin tashin jirage na Benin shi yasa aka tsare shi don bincike
  • Kawo yanzu dai a hukumance, hukumar kula da sufirin jirage, NCAA, ba ta yi tsokaci kan tsare jirgin dan takarar shugaban kasar na LP ba

Bayyana sun fito a ranar Alhamis kan dalilin da yasa aka tsare jirgin saman dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, Peter Obi, da Hukumar kula da sufurin jiragen sama, NCAA, ta yi.

Shugaban sashin watsa labarai na kamfen din Obi-Datti, Mista Diran Onidade, cikin sanarwar da ya fitar ya koka kan lamarin, yana mamakin 'tsare jirgin su da aka yi ba tare da bayani ba.'

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Peter Obi
Dalilin Da Ya Sa NCAA Ta Tsare Jirgin Kamfen Din Peter Obi - Majiya. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce matakin ya janyo wasu jami'an jam'iyyar da suka taru a filayen jiragen Legas da Abuja, sun gaza zuwa kamfen din da aka yi a Ibadan.

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa jirgin saman mai lamba 5Y-HPY kirar Bombardier DHC-8-400 mallakar DAC Aviation ne mai bada haya.

Dalilin da yasa NCAA ta tsare jirgin kamfen din Peter Obi - Majiyoyi

Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust a ranar Alhamis cewa an tsare jirgin ne saboda saba ka'idojin tsaron lafiya ta hanyar saba umurnin jami'an kula da zirga-zirgan jirgi na cewa kada su bar filin jirgi na Benin.

An gano cewa hukumar kula da jiragen ta fara bincike kan lamarin yayin da jirgin ya ke a tsare, Pulse NG ta rahoto.

Wata majiyar daban ta ce:

Kara karanta wannan

"Mazi Tinubu": Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC Ya Samu Sarauata A Yankin Su Peter Obi

"Wannan ba shi da alaka da siyasa kuma NCAA ba ta lamuntar saba dokoki. Akwai dokoki sosai a bangaren sufurin jiragen sama saboda rayukar mutane ake harka da su."

NCAA ba ta ce komai ba a hukumance kan lamarin duba da cewa shugabanta, Kyaftin Musa Nuhu, bai riga ya amsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada rahoton.

Daily Trust ta rahoto cewa wasu tsirarun filayen jiragen sama na kasa da kasa kamar na Abuja, Legas, Kano da Enugu suna aiki na awa 24 amma irin na Benin da Ibadan suna aiki daga fitowar rana zuwa faduwarta ne.

Dalilai 5 Da Za Su Iya Hana Peter Obi Cin Zaben 2023 - Fitch Solutions

Akasin bayanai da ke fitowa, binciken Fitch Solutions ya nuna cewa, dan takaran kujerar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi zai fadi a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gobara Ta Tashi A Tashar Mota A Shahararriyar Jihar Arewa, An Tafka Asara

kamfanin Fitch Solutions, a rahoton binciken da ya fitar, ya bayyana dalilan da ya ka iya hana Peter Obi cin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel