"Mazi Tinubu": Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC Ya Samu Sarauata A Yankin Su Peter Obi

"Mazi Tinubu": Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC Ya Samu Sarauata A Yankin Su Peter Obi

  • Bola Tinubu na cigaba da fadada yakin neman zabensa a yankunan kasar a kokarinsa na zama shugaban kasa a 2023
  • Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya tafi jihar Ebonyi yin kamfen a kudu maso gabashin Najeriya
  • A wani irin tarba ta arziki da aka masa, an bawa Tinubu saurautar "Dike Di Ora Nma I" na jihar Ebonyi

Ebonyi, Abakaliki - An bawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, sarauta a jihar Ebonyi.

An bawa tsohon gwamnan na jihar Legas dan shekara 70 sarautar "Dike Di Ora Nma I" a jihar Ebonyi a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba.

Mazi Tinubu
"Mazi Tinubu": Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC Ya Samu Sarauata A Yankin Peter Obi. Hoto: @BashirAhmaad.
Asali: Twitter

Bashir Ahmad, mataimaki na musamman kan sadarwa ta zamani ga shugaban kasa kuma mataimakin direkta, kafafen watsa labarai na musamman na kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC, ya tabbatar da hakan a rubutun da ya yi a dandalin sada zumunta da Legit.ng Hausa ta gani.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Jerin Manyan Jiga-jigan APC 6 Da Basa Goyon Bayan Tinubu Saboda Tikitin Musulmi da Musulmi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya yi wa hoton lakabi da:

"Ku sadu da Dike Di Ora Nma I na jihar Ebonyi, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu."

Masu amfani da dandalin sada zumunta sun magantu, sun ragargaji Tinubu

A bangare guda, wasu yan Najeriya ba su ji dadin wannan cigaban ba yayin da suke kwatanta hakan da lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yakin neman zabe.

Wasu masu adawa sun bayyana abin a matsayin wani yunkuri na tallata kansa duk da irin wahalhalun da jam'iyyar APC ta jefa yan Najeriya ciki a shekaru bakwai da suka gabata.

@Dennismart_one ya ce:

"Haka kuma rude mu da Buhari. Ya Allah, wane muka yi wa laifi? Ko da ta hanyar wannan wallafar ka ke cin abinci, duk da haka."

@DavidHarts2 ya ce:

"Dike di Chad mma.

Kara karanta wannan

2023: APC ta samu karin karfi, wasu jiga-jigan sarakuna sun ce suna goyon bayan Tinubu

"Mutumin da ya yi alkawarin zai cigaba da bada albarkatun kasar mu ga kasashen waje - kamar Buhari, a maimakon fuskantar matsalolin da ke adabar mu.
"Mutumin da ya yi alkawarin zai yi aiki a Tafkin Chadi, yayin da ya yi watsi da matsalolin mu."

@Eber_Di_Maria ya ce:

"Yanzu ya zama cikakken mamba na kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biafra IPOB, ko ba haka ba?"

2023: Bola Tinubu Ya Yi Tuntuben Harshe, Ya Ce Allah Ya Albarkaci PD....APC, Bidiyo Ya Bazu

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi tuntuben harshe yayin da yake jawabi a wurin kaddamar da kamfen dinsa a jihar Filato.

Gangamin taron ya gudana ne a a babban filin Rwang Pam township stadium, da ke Jos, babban birnin jihar Filato ranar Talata kamar yadda The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel