Dalilai 5 Da Ka Iya Hana Peter Obi Samun Nasara A Zaben 2023, Fitch Solutions

Dalilai 5 Da Ka Iya Hana Peter Obi Samun Nasara A Zaben 2023, Fitch Solutions

Sabanin abinda ake radawa, bincike Fitch Solutions ya nuna cewa Peter Obi, dan takaran kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party LP zai sha kaye a zaben 2023.

A rahoton binciken da kamfanin Fitch Solutions ya fitar, ya bayyana dalilan da ya ika hana Peter Obi samun nasara a karshe.

Fitch Solutions wani sashe ne na kamfanin Fitch Ratings dake da zama a birnin New York, kasar Amurka.

1. Peter Obi bai da goyon bayan Musulman Arewa

A cewar rahoton, Peter Obi, ba zai samu kuri'un mabiya addinin Islama ba wadanda sune masu rinjaye a Arewacin Najeriya.

Dalilin haka shine akwai sauran yan takara biyu masu karfi duk Musulmai ne.

2. Jam'iyyarsa ba tada Sojoji yakin neman zabe a ko ina

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya kara da cewa jam'iyyar Labour Party bai da Sojojin yakin neman zabe a wasu jihohin Najeriya.

"Musamman jam'iyyar ba tada yan takaran kujerun majalisar jiha, majalisar wakilai, majalisar dattawa da kuma gwamna," cewar rahoton.

3. Obi Na bukatar kashi 25% na kuri'un jihohi 24

Bisa kundin tsarin mulkin Najeriya, dan takarar kujerar shugaban kasa na bukatar samun akalla kashi 25% na kuri'un jihohi 24 kafin a sanar shi ya lashe zabe.

Sakamakon rashin mabiya a jihohi da yawa, rahoton Fitch yace da kamar wuya Obi ya samu nasara.

4. Gwamnonin Kudu Maso Yamma, Kudu maso kudu da Kudu Maso gabas basu tare da shi

Duk da cewa shi dan kudu ne, Peter Obi bai wani gwamna a dukkan yankunan kudu uku dake tare da shi.

Yayinda Gwamnonin kudu maso yamma suka bayyana karara cewa dan takaran APC zasu zaba, na kudu maso kudu sunce ba si tare da shi, hakazalika na yankinsa kudu maso yamma.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru

5. Masoya Peter Obi a yanar gizo kawai suke

Rahoton Fitch yace duk zabukan yanar gizo dake nuna Peter Obi zai samu nasara almara ne.

Ishara ga wani rahoton bankin duniya na 2020, Fitch yace kashi 36% kacal na yan Najeriya ke amfani da yanar gizo.

Yace:

"Zabukan jin ra'ayi dake nuna Obi zai kada Bola Tinubu (APC) da Atiku Abubakar (PDP), duk na yanar gizo ne."
"Tun da kashi 36% na yan Najeriya ke amfani da yanar gizo (World Bank 2020), muna ganin mazauna birane masu kudi ne ke goyon bayan Obi."

Mafi akasarin wadanda zasu kada kuri'a ranar zabe basu yanar gizo

Asali: Legit.ng

Online view pixel