‘Yan Majalisa Za Su Fara Binciken ‘Son Kai’ da Aka Yi Wajen Daukar Ayyuka a Gwamnati

‘Yan Majalisa Za Su Fara Binciken ‘Son Kai’ da Aka Yi Wajen Daukar Ayyuka a Gwamnati

Majalisar wakilan tarayya za tayi bincike kan ayyukan da aka ba mutane a NUPRC da NEITI

‘Yan majalisa suna zargin ba ayi adalci wajen raba aikin ba, an fifita wani bangaren kasar nan

Kwamitocin majalisa za suyi bincike biyo bayan korafin da Hon. Hafizu Ibrahim Kawu ya yi

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta yanke hukuncin yin bincike a kan zargin rashin adalcin da aka yi wajen daukar mutane aikin gwamnatin Najeriya.

Jaridar Premium Times a rahoton da ta fitar, tace an dauki aiki a ma’aikatun NEITI da NUPRC, inda aka yi son-kai wajen fifita wani bangaren kasar nan.

Honarabul Hafizu Ibrahim Kawu mai wakiltar mazabar Tarauni a majalisar wakilan tarayya ya bijiro da wannan a wani zama da aka yi a ranar Laraba.

A rahoton da ya zo a Daily Trust, ana zargin cmutum 21 daga cikin sababbin ma’aikatan da aka dauka a NEITI daga Kudu maso gabas suka fito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban NEITI na kasa, Ogbonnaya Orji ya maida martani ga rahoton. yana cewa ma’aikatarsa ta samu cikakken izinin hukumar FCC kafin ta dauki aikin.

Orji yace sun dauki aikin ne a dalilin tarin mutanen da suka nuna sha’awar aiki da su.

‘Yan Majalisa
Majalisar Wakilan Tarayya Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: Twitter

An saba ka'ida - Hon. Kawu

Da ya tashi a zauren majalisar wakilai, Hafizu Ibrahim Kawu yace daukar aikin da aka yi a ma’aikatun nan biyu sun jawo surutu domin a nuna adalci ba.

Hon. Kawu yake cewa NEITI da NUPRC sun sabawa sashe na 14(3) na kundin tsarin mulkin kasa wanda yace ma’aikatu su guji nuna bambanci a ayyukansu.

Kundin tsarin mulkin ya yi haka domin tabbatar da hadin-kai tsakanin mabambantan al’ummu.

Bai halatta gwamnatin tarayya ko wata ma’aikata ko kuwa hukumarta, ta rika gudanar da ayyukanta ta hanyar kebe daidaikun jihohi ko wata kabila ba.

Kwamitoci za suyi bincike

Ba tare da wata doguwar muhawara ba, The Cable tace ‘yan majalisan tarayya suka gamsu da abin da Hon. Kawu ya fada, suka mara masa baya a kan korafin.

Idan ta tabbata an yi son-kai, majalisa za ta bukaci a soke daukar aikin da aka yi. Tuni aka bukaci kwamitocin da abin ya shafa suyi bicike na musamman.

Rikicin VAT a jihohi

An samu labari cewa shekarar nan, Ribas ta samu N321bn wanda N112bn sun fito ne daga IGR, Nyesom Wike yana so kudin shigan su karu ta hanyar karbar VAT

Gwamnan na PDP ya yi kira da babban murya ga duk wani Gwamna ya taimaka wajen ganin ya yi nasara a kan gwamnatin tarayya a shari'ar da yake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel