Gwamna Wike Yana Zugo Gwamnoni 36 Su Taya shi Yaki da Gwamnatin Najeriya kan Haraji

Gwamna Wike Yana Zugo Gwamnoni 36 Su Taya shi Yaki da Gwamnatin Najeriya kan Haraji

  • Nyesom Wike bai hakura da maganar kyale Gwamnoni su rika karbar harajin VAT a jihohinsu ba
  • Gwamnan ya gabatar da N420bn a matsayin kasafin kudin da Ribas za ta kashe a shekara mai zuwa
  • Wike ya yi wannan lissafi ne har da VAT da Gwamnatin Ribas za ta karba, duk da shari’ar tana kotu

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike yana nan a kan maganar canza tsarin haraji, ta yadda gwamnoni za su rika karbar harajin VAT a jihohinsu.

Nyesom Wike ya yi kira ga sauran Gwamnonin kasar nan, da su taimakawa Ribas wajen ganin jihohi sun karbe iko da harajin kayan masurufi na VAT.

Daily Post tace Mai girma Gwamnan ya yi wannan kira ne a lokacin da ya gabatar da kasafin kudin Ribas na shekarar 2023 a gaban ‘yan majalisar dokoki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Zubar Da Hawaye Yayin Da Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Karshe A Matsayin Gwamna

Da yake jawabi a ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba 2022, Gwamnan yace kasafin kudin na 2023 ya yi la’akari da kason da Ribas za ta samu daga VAT.

Wike ya fara samun nasara a kotu

Ganin Alkalin kotun tarayya ya zartar da hukunci cewa jihohi ke da iko da wannan haraji a Najeriya, Gwamnan ya fara lissafi da kudin a cikin baitul-mali.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yanzu maganar tana gaban kotun koli, inda za a raba gardama tsakanin bangarorin biyu.

GovWike
Gwamna Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Wike ya yi wa ‘yan majalisar jiharsa bayanin cewa abin da gwamnatin Ribas za ta kashe a shekara mai zuwa, ya ta’allaka da hukuncin da kotun koli tayi.

Rahoton yace Gwamnan ya jaddada cewa zai dage wajen ganin ya bunkasa kudin shiga ta hanyar jawo masu hannun jari, bude kamfanoni da gyara haraji.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Atiku Zai Yi Sulhu Da Boko Haram? Ɗan Takarar Na PDP Ya Bayyana Abinda Ke Zuciyarsa

Abin da ya fadawa Majalisa

“Za mu cigaba da zage dantse wajen kokarin mu na kara kudin-shigan da muke samu ta hanyar kawo damammaki, shigo da hannun jari, kamfanoni da gyara karbar haraji.
Duk da ba mu kai ga inda muke hari ba, amma ba za muyi kasa a gwiwa ba a nufinmu na rage dogaron da jihar mu tayi da gwamnatin tarayya wajen tsara kasafin kudinta.
Muna kira ga sauran takwarorinmu jihohi da su bamu gudumuwa wajen wannan gwagwarmaya domin samun damar yankewa da karbar harajin VAT a matakai na jihohi.”

- Nyesom Wike

This Day tace gwamnan ya nuna tun tuni akwai bukatar a canza yadda ake rabon arziki, yace gibin da ake samu a kasafin kudi a dalilin karancin haraji ne.

Wike ya jinjinawa Buhari

Kwanan nan aka samu rahoto Gwamna Nyesom Wike ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta biya jihohin Neja-Delta kudin da suke bin bashi.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Tsinci Kansa A Matsala Kan Sukar Peter Obi, Matasan Ibo Sun Bayyana Matakin Da Za Su Ɗauka A Kansa

Akwai 13% da ake warewa Jihohin masu arzikin fetur, wanda Gwamnoni suke bin gwamnatin tarayya, bayan an dade ana sauraron kudin, yanzu sun fito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel