Shugaba Buhari Ya Kaddamar da Rijiyar Man Fetur Ta Farko da Aka Haka a Arewa

Shugaba Buhari Ya Kaddamar da Rijiyar Man Fetur Ta Farko da Aka Haka a Arewa

  • Yankin Arewacin Najeriya kafa tarihi a yau 22 ga watan Nuwamban 2022 yayin da Buhari ya kaddamar da mahakar mai na yankin
  • An jima ana yiwa yankin Arewa kallon ci man zaune yayin da jihohin Kudu maso Gabas ke samar da man fetur ga tattalin arzikin kasar
  • Rahoto ya ce, mahakar man Kolmani za ta samar da danyen mai da ya kai ganga biliyan daya

Arewa maso Gabas - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci manyan masu ruwa da tsaki wajen kaddamar da mahakar mai ta garin Kolmani da ke tsakanin jihohin Gombe da Bauchi, The Nation ta ruwaito.

Wannan mahaka ta Kolmani ita ce ta farko a Arewacin Najeriya, lamarin da ‘yan yankin ke alfahari dashi tun farkon da Buhari ya fara aikin a shekarun baya.

Kara karanta wannan

Ana Neman Sabun Sabani Tsakanin Gombe da Bauchi kan Mallakar Danyen Mai a Arewa

Akalla yanzu shekaru biyu kenan da aka gano man fetur da ke dankare a yankin, wanda gwamnati ta ba da aikin hako shi cikin gaggawa.

Baya ga rijiyoyin mai da ake dasu a Kuduncin Neja Delta, wannan yanki shine na farko a Arewa, baya ga wanda aka fara aka gaza nasara a jihar Borno saboda rashin tsaro.

Buhari ya kaddamar da mahakar mai ta farko a Arewa
Shugaba Buhari Ya Kaddamar da Rijiyar Man Fetur Ta Farko da Aka Haka a Arewa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

NNPC ta fara aikin bankado danyen mai a Arewacin Najeriya, inda suka gano akwai adadi mai yawa a jihohin Gombe, Bauchi, Borno da Neja.

Fa'idar wannan mahakar mai ga Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa, mahakar Kolmani zata cike gurbin ganga akalla biliyan daya na adadin man ma'ajiya na Najeriya, wanda ya gaza motsawa zuwa sama kusan shekaru 10 kenan yanzu, Daily Trust ta ruwaito.

Wadanda suka halarci wannan kaddamarwa sun hada da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, gwamna Bala Muhammad na Bauchi, Inuwa Yahaya na Gombe, Simon Lalong na Filato, Atiku Bagudu na Kebbi da Abubakar Badaru na Jigawa.

Kara karanta wannan

Yayinda Buhari Ke Shirin Kaddamar Da Aikin Hako Mai A Bauchi, Jama'ar Alkaleri Sun Gabatar da Bukatunsu

Hakazalika, gwamna Buni na Yobe ya halarta tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

Sauran sun hada da ministan sadarwa Pantami, ministan shari’a Malami, ministan man fetur Timipre Sylva, ministar masa’anatu Hajiya Maryam Katagum da shugaban NNPC, Dr Mele Kyari da dai sauransu.

Duk da samun wannan mai a Arewa, jihohin Bauchi da Gombe na gab da shiga sabani saboda tunanin a wacce jiha ce takamaimai aka samu wannan alheri.

Rahoton da muka kawo a baya ya bayyana yadda aka fara kai ruwa rana kan wannan lamari tun kafin a je ko'ina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel