Dakarun Sojoji Sun Sheka ‘Yan Ta’addan Boko Haram 5, Sun Kama 1 Da Ransa a Borno

Dakarun Sojoji Sun Sheka ‘Yan Ta’addan Boko Haram 5, Sun Kama 1 Da Ransa a Borno

  • Rundunar sojojin Najeriya ta yi gagarumin nasara a yaki da take yi da masu tayar da kayar baya a arewa maso gabashin kasar
  • Dakarun Operation Hadin kai sun murkushe mayakan kungiyar ta’addanci biyar sannan suka kama daya dan ransa a jihar Borno
  • Sojojin sun farmaki yan Boko Haram din ne bayan samun bayana sirri kan shige da ficensu

Borno - Dakarun Operation Hadin kai da ke yaki da ta’addanci a yankin kudu maso gabas, sun kashe mayakan Boko Haram biyar sannan suka kama daya da ransa a jihar Borno.

Zagazola Makama, wani kwararre kan tsaro a tafkin Chadi, ya rahoto cewa dakarun rundunar sojin Najeriyan sun yi gagarumin nasarar ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, bayan sun yi aiki kan bayanan sirri.

Jihar Borno
Dakarun Sojoji Sun Sheka ‘Yan Ta’addan Boko Haram 5, Sun Kama 1 Da Ransa a Borno Hoto: The Cable
Asali: UGC

Bayanan da suka samu na sirri sun nuna cewa wasu masu tayar da kayar baya na yawo daga arewacin borno zuwa yankin Mafa.

Kara karanta wannan

Hotuna Daga Shagalin Bikin Jarumar Kannywood, Halima Atete, Jama'a Sun Yi Martani

Wasu majiyoyi na sirri sun fadama Zagazola Makama cewa dakarun sun kai kautan bauna kan yan ta’addan kuma nan take suka kashe biyar daga cikinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyin sun bayyana cewa an mika dan ta’addan da aka kama zuwa ga hannun dakarun soji don gudanar da bincike.

A cewarsa, dakarun soji na mamaye yankin a yanzu haka inda suka yin faturol mai zafi da kuma bibiyar sauran yan ta’addan don gano su da kuma kashe su.

Yan sa-kai sun halaka mayakan Boko Haram uku

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa jami'an sa-kai sun yi nasarar halaka mayakan Boko Haram guda uku a yankin Konguna da ke jihar Borno.

Yan sa-kan sun kaiwa mayakan kungiyar ta'addancin kautan bauna yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa karbar kudin fansar wani mutumi da suka yi garkuwa da shi daga hannun danginsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Tsinci Kansa A Matsala Kan Sukar Peter Obi, Matasan Ibo Sun Bayyana Matakin Da Za Su Ɗauka A Kansa

Bayan sun harbe su, biyu sun mutu ne a nan take inda aka gano gawar cikon na ukunsu a wani wuri daban. An kuma yin nasarar kwato babur da wasu makamai daga wajen yan ta'addan.

Har ila yau, sojojin sun yi nasara kan wasu yan ta'adda a yankin Bama da ke jihar ta Borno bayan sun yi masu ruwan bama-bamai a mabuyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel