Kannywood: Shagalin Bikin Jaruma Halima Atete Ya Kankama, Hotuna Sun Yadu

Kannywood: Shagalin Bikin Jaruma Halima Atete Ya Kankama, Hotuna Sun Yadu

  • An fara gudanar da shagulgulan bikin jaruma Halima Atete da Angon Mohammed Mohammed Kala
  • Tuni hotunan kasaitacciyar liyafar da aka yi a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba suka karade shafukan soshiyal midiya
  • Masu amfani da shafukan soshiyal midiya sun taya jarumar ta Kannywood murna inda suka yi mata addu'an samun zaman lafiya na har abada

Borno - Shagalin biki ya kankama na auren shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Halima Atete.

Za dai a daura auren kyakkyawar jaruma Halima Atete da hadadden angonta mai suna Mohammed Mohammed Kala a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba, a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Biokin Atete
Kannywood: Shagalin Bikin Jaruma Halima Atete Ya Kankama, Hotuna Sun Yadu Hoto: Kannywoodcelebrities
Asali: Facebook

An gudanar da wata ‘yar kwarya-kwaryar liyafa a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba inda amarya ta fito shar da ita cikin ado na manyan mata.

A cikin wani dakin taro da aka kawata da kayan kyale-kyale, an gano amarya Halima zaune cikin shiga ta kamala sannan jikinta lullube na mayafi wanda ke kara fito da zatinta na ‘ya mace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun a bara dai matan masana’antar fim din suka fara baiwa marada kunya ta hanyar share bakin fentin da ka masu na cewar basa son yin aure.

Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya ce ta fara bude fagen kuma bayan ita an yi wasu da dama inda na baya-bayan nan da aka yi shine na Rukayya Umar Santa wacce aka fi sani da Dawayya.

Dawayya dai ta amarce ne da shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano, Na’abba Afakalla.

Ga hotunan shagalin wanda shafin Kannywoodcelebrities ya wallafa a Facebook:

Jama’a sun yi martani tare da taya jarumar murna

Muhammed Soja Lk ya yi martani:

“Allah.. Ya. Bada.. za malafiya.”

Abdullah Sale ya ce

“Allah make roko yabaki zaman lfy mai daurewa.”

Abdul Adam ya yi martani:

“Angon bazai samu damar zuwa ba kenan kodai shima auran dole akayi Masa ne?”

Basiru Usman Majidadi ya ce:

“Duk irin su daya da 'yan uwan ta Allah yasa alkhairi ya basu zaman lfy.”

Bint Mahmuod

“Allah ubangiji ya bata ikon zama gidan mijinta. Aamin ya Rabbi. Don su yan film dinnan bayin auren ba, zaman ne.”

Sahal Aliyu Rahama ya ce:

“Allah ya sa gidan zama ne na har abada.”

Umar Rabiu Kirki ya rubuta:

“Allah Sarkin Allah yasanya alkairi Allah ya bada zaman lafiya atete.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel