Yan Sa-Kai Sun Murkushe Mayakan Boko Haram Uku a Jihar Borno

Yan Sa-Kai Sun Murkushe Mayakan Boko Haram Uku a Jihar Borno

  • Mayakan kungiyar Boko Haram uku sun hadu da ajalinsu a karamar hukumar Konguno a jihar Borno
  • Yan bijilanti sun kaiwa yan ta’addan harin bazata a hanyarsu ta zuwa wurin karbar kudin fansar wani da suka sace
  • Lamarin da ya afku a yammacin ranar Lahadi, ya yi sanadiyar kwato makamai da babur daga hannun masu tayar da zaune tsayen

Borno - Kungiyar yan bijilanti da ke da goyon bayan gwamnati sun kai harin kwantan bauna kan mayakan kungiyar ta’addanci a yankin karamar hukumar Konguno ta jihar Borno.

Kamar yadda gidan talbijin na AIT ya rahoto, yan sa-kan sun yi nasarar murkushe mayakan Boko Haram uku a harin.

Jihar Borno
Yan Sa-Kai Sun Murkushe Mayakan Boko Haram Uku a Jihar Borno Hoto: TheCable
Asali: UGC

Mayakan na hanyar zuwa karbar kudin fansa

An tattaro cewa yan bijilanti din sun kama tare da bindige biyu daga cikin yan bindigar a hanyar su ta zuwa karban wasu kudade na kudin fansa daga iyalan wani mutum da suka yi garkuwa da shi a yammacin ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

2023: Wani Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Fara Zawarcin Yan Arewa, Ya Musu Alkawarin Kawar da Talauci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zagazola Makama ya samo daga majiya abun dogaro cewa an tsinci gawar daya daga cikin yan ta’addan da ya tsere da raunuka daga bisani.

Majiyoyi sun bayyana cewa an kuma kwato makamai da babur a daga wajen masu tayar da kayar bayan.

Sojoji sun murkushe yan bindiga a Borno

A wani labari makamancin wannan, dakarun rundunar soji sama sun yi yayyafin wuta a mabuyar kungiyar ta’addanci da ke garin Banki a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, lamarin da ya kai ga murkushe mayaka da dama.

Rahotanni sun nuna akalla mayakan kungiyar ta’addanci 16 ne suka halaka yayin da jirgin NAF yayi masu ruwan bama-bamai mafakar yan ta'addan da ke Chongolo da Tangalanda.

Sojojin sun kai samamen ne bayan sun samu bayanan sirri da ke tabbatar da kasancewar yan ta’addan a wajen.

Kara karanta wannan

Dakarun Soji Sun Murkushe Yan Boko Haram Da Dama Bayan Yi Masu Yayyafin Wuta a Borno

Legit.ng ta kuwa kawo a baya cewa dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe wasu kasurguman yan ta'adda uku da ake nema idanu a rufe a jihar Zamfara.

A wani samame da suka kai jihar, hazikan sojin sun murkushe Alhaji Gana, Halilu Buzu da kuma Yellow Kano tare da kuma wasu mayakan kungiyar ta'addanci da dama a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel