Sarkin Kano Ya Yabi Muhimmin Aikin Buhari 1 da Zai Bunkasa Tattalin Arzikin Arewa

Sarkin Kano Ya Yabi Muhimmin Aikin Buhari 1 da Zai Bunkasa Tattalin Arzikin Arewa

  • Mai martaba Aminu Ado Bayero ya yaba da aikin AKK da Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo
  • Sarkin Kano yana ganin za a taimaki Arewa da daukacin ‘Yan Najeriya idan aikin nan ya tabbata a nan gaba
  • Shugabannin kamfanin NNPC da Brentex CPP Limited sun kai wa Aminu Ado Bayero wata ziyara a fadarsa

Kano - Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yabi aikin AKK da ake yi a matsayin wani cigaba da za a samu a bangaren tattalin arziki da walwalar al’umma.

This Day ta rahoto yana bayanin yadda wannan aiki na shimifida bututun gas na Ajaokuta-Kaduna- Kano zai taimaki Arewacin Najeriya.

Mai martaba Aminu Ado Bayero ya gabatar da jawabi a sa'ilin da tawagar kamfanin NNPC Limited da na Brentex CPP Limited suka kawo masa ziyara.

Kara karanta wannan

Najeriya Za Ta Samu Naira Tiriliyan 32 Daga Rijiyoyin Man da Aka Samu a Yankin Arewa

Sarkin Kano yace aikin da ake yi na musamman ne, sannan ya yi amfani da wannan dama ya yi kira ga kamfanin ya tabbatar ya karasa shimfida bututun.

"Babu bukatar a tsaya nanata muhimmancin wannan aiki. Muna sa ran idan an kammala kwangilar, za tayi sanadiyyar bunkasar tattalin yankin da na Najeriya baki daya."

- Aminu Ado Bayero

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin AKK
Aikin shimfida bututun AKK Hoto: marineandpetroleum.com
Asali: UGC

Babba Dan’ Agundi shi ne Shugaban aiki

Rahoton yace shugaban NNPC-AKK na shiryyar Kano, Aminu Babba Dan’Agundi ya gabatar da ‘yan kwamitinsa gaban Mai martaba Sarkin a cikin fadarsa.

Sarkin Dawaki Babba ya yi godiya ga gwamnatin tarayya da ta kawo masu wannan aiki.

Daily Trust tace babban Darektan ayyuka na kamfanin NGIL da ke karkashin NNPC Limited, Audu Ibrahim ya jagaoranci tawaga zuwa fadar Sarkin a Kano.

Audu Ibrahim ya ji dadin irin goyon bayan da suka samu daga wajen Mai martaba, Aminu Bayero.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Buhari ya kaddamar da mahakar man fetur ta farko a jihohin Arewacin Najeriya

Shi kuma Sani Nuhu Abubakar, a matsayinsa na mataimakin shugaban Brentex CPP Limited, ya yabi Mallam Mele Kolo Kyari da ya bada damar yin aikin.

Wike da shari'ar VAT

Rahoto ya zo cewa Gwamna Nyesom Wike ya yi kira da babban murya ga duk wani Gwamna ya taimaka wajen ganin ya yi nasara a kan gwamnatin tarayya.

Gwamnatin Ribas tayi karar Gwamnatin tarayya domin a ba jihohi damar karbar harajin VAT, shari’a tana kotu a yanzu, amma Wike yana sa ran yin nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel