Najeriya Za Ta Samu Naira Tiriliyan 32 Daga Rijiyoyin Man da Aka Samu a Yankin Arewa

Najeriya Za Ta Samu Naira Tiriliyan 32 Daga Rijiyoyin Man da Aka Samu a Yankin Arewa

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace akwai fiye da gangunan danyen mai Biliyan 1 a Kolmani
  • A sanadiyyar wannan arziki, Mai girma Muhammadu Buhari yace ‘yan kasuwa sun narka jarin $3bn
  • Rijiyoyin man Kolmani za su jawo Naira Tiriliyan 32 suka shiga asusun tarayya idan aka fara hako mai

Bauchi - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa hako danyen mai da aka fara yi a rijiyoyin Kolmani ya jawo ‘yan kasuwa za su narka Dala biliyan 3.

Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wannan bayani a lokacin da za a fara aikin hako man a ranar Talatar nan. Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoton nan.

Baya ga hannun jarin da ‘yan kasuwa suka zuba, shugaban kasar ya bayyana cewa ana cigaba da kokarin gano rijiyoyin mai a yankin Anambra da Benuwai.

Kara karanta wannan

Tinubu: Buhari ya jefa Najeriya a yunwa, amma ya yi wani abu 1 da ya kamat kowa ya sani

Wannan yana cikin yunkurin kamfanin NNPP na tono danyen mai a yankunan Anambra, Dahomey, Sokoto, zuwa lardin Benuwai da tafkin Chad da Bida.

Arziki ya bayyana a Arewa

A yankin Kolmani, shugaban kasa ya tabbatar da cewa akwai fiye da ganguna biliyan 1 na danyen mai da taku biliyan 500 na arzikin gas da a a fara morarsu ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton yace a dalilin haka, an kwadaito da ‘yan kasuwa sun zuba hannun jarin Dala biliyan 3 a aikin. Hakan ya zo sa’ilin da ‘yan kasuwa ke ja baya da mai.

Buhari
Muhammadu Buhari a Kolmani Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

N32tr a cikin shekaru 10

A wani rahoton na Daily Trust har ila yau, an ji cewa rijiyoyin man OPL 809 da kuma 810 za suyi sanadiyyar da Najeriya za ta samu fiye da Naira tiriliyan 30.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Buhari ya kaddamar da mahakar man fetur ta farko a jihohin Arewacin Najeriya

La’akari da farashin da ake saida gangar danyen mai a kasuwar Duniya, Najeriya za ta samu $73b (kusan N32.3tr) daga rijiyoyin Kolmani cikin shekaru goma.

A halin yanzu an yi lissafin za a saida kowace gangar danyen mai a kan Dala $73. A wasu lokutan farashin ya kan bambanta da yadda gwamnati tayi kasafi.

Za a samu wannan kudi ne daga lokacin da aka fara hako danyen man, ana saidawa a kasuwa.

Gwamnonin Bauchi da Gombe sun yi alkawarin za su taimaka wajen bada hadin-kai domin ganin aikin harko man ya tabbata, ba tare da an samu matsaloli ba.

Barazanar tsaro a Najeriya

An samu labari cewa bayanin Manjo Hamza Al-Mustapha ya nuna shigowar manyan makamai da kwayoyi sun karu, kuma an rasa daga ina ake shigo da su.

Idan ba a dauki mataki ba, barkowar makamai zai iya zama barazana ta fuskar zaman lafiya ga zaben da ake sa ran za a gudanar a farkon shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Ta tabbata: An kaure tsakanin 'yan Kudu da Arewa a Twitter bayan gani hotunan man da aka hako a Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel