Kano: Akan Idanunmu ‘dan Chana Ya Damuki Ummita, Ya Burma Mata Wuka a Wuya, Kanwar Ummu

Kano: Akan Idanunmu ‘dan Chana Ya Damuki Ummita, Ya Burma Mata Wuka a Wuya, Kanwar Ummu

  • Asiya Sani Buhari, kanwar UmmuKulsum Buhari, budurwar da saurayinta ‘dan Chana ya halaka a Kano ta bada labarin yadda lamarin ya kasance a gaban kotu
  • Ta sanar da cewa, daga mahaifiyarmu ta budewa ‘dan Chanan kofa, ya shigo tare da damkar Ummu ya shige dakinta ya garkame kofa
  • Tace suna leke ta tagar dakin tare da mahaifiyarta yadda ya damuketa ya kai ta gado tare da fitar da wuka, hakan yasa ta fara bashi hakuri amma ya soka mata a wuya

Kano - Asiya Sani, kanwar Ummulkulsum Buhari, wacce ake zargin saurayinta ‘dan kasar Chana mai suna Geng Quanrong ya halaka, a jiya Laraba ta sanar da babban kotun dake zama a Kano cewa ido da ido ta ga lokacin da Geng ya sokawa ‘yar uwarta wuka.

Kara karanta wannan

Matata Ta Zuba Mun Guba Kuma Bata Ganin Girma Na, Miji Ya Nemi Kotu Ta Raba Aurensa

Kotun Kano
Kano: Akan Idanunmu ‘dan Chana Ya Damuki Ummita, Ya Burma Mata Wuka a Wuya, Kanwar Ummu. Hoto daga Vanguardngr.news
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, Asiya ta bayyana hakan ne yayin da ta bayyana gaban kotu domin bada shaida kan shari’ar da ake yi.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Geng ya musanta kisan tsohuwar budurwarsa wacce yanzu marigayiya ce.

Yadda Geng ya damuki Ummu, Asiya

Tace ta leka ta taga kuma ta ga yadda ya damuki ‘yar uwarta a kan gado tare da sharba mata wuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda tace:

“A wannan ranar, 16 ga watan Satumban 2022 wurin karfe 9 na dare, ‘dan Chanan yazo yana buga mana kofar gida. Naje budewa ne ‘yar uwarta Ummu ta dakatar da ni. Na fada mata ba zamu cigaba da zama yana buga mana kofa ba yana damun mu tare da makwafta.
“Ta sanar da mahaifiyarmu cewa tana da damar hana shi zuwa gidanmu.
“Mahaifiyarmu tana bude kofar ya hanzarta shigowa gidanmu. A yayin da ya shigo, Ummu ta cewa mahaifiyarmu kin ga ya shigo ko? Bari in kira ‘yan sanda su kama shi. Tana shiga dakin ne ya bi ta tare da rufe kofar.”

Kara karanta wannan

2023: Buhari ya fadi abin da zai faru idan PDP ko wata jam'iyya ta lashe ba Tinubu ba

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa, Asiya ta cigaba da cewa:

Mun leka ta taga, Cewar Asiya

“Mun fara leke ta taga kuma mun ga yadda yake damukarta. Mun dinga ihun neman taimako. Ya fito da wuka, a nan ne Ummu ta fara rokonsa. Kafin makwabcinmu Mustapha ya dira ta tagar, ya soka mata wuka. A take na ga jini yana fitowa daga wuyan Ummu.”

Asiya cike da takaici ta cigaba da bayyana cewa:

“Geng ya fito ta tagar zuwa falo. Sai ya hanzarta fita daga gidan. Daga nan ne makwabtanmu suka fara shigowa gidanmu tare da yunkurin kai ta asibiti. An shawarcemu da mu jira ‘yan sanda.
“Lokacin da Surajo, Abdulsalam da ni muka kai ta asibiti, bata iya ko motsi. Mun kai ta UMC kuma likitan dake aiki ya bukaci sanin abinda ya faru, mun sanar cewa wuka aka soka mata.
“A yayin da nake jira ne na karasa ofishin likitan kuma na ga Surajo da Sadiq inda likita ya tabbatar mana da cewa Ummu ta rasu.”

- Asiya ta fadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel