An Tasa Keyar Fasto Gidan Yari Bisa Zargin Damfarar Malamin Makaranta N3m

An Tasa Keyar Fasto Gidan Yari Bisa Zargin Damfarar Malamin Makaranta N3m

  • Kotu ta tasa keywar wani fasto zuwa magarkama bisa zargin ya ci kudin wata malamar makaranta a jihar Legas
  • An kamo faston ne bayan da ya gudu, inda dan sanda mai gabatar da kara ya bayyana dalla-dalla abin da ya faru
  • Fasto ya musanta zargin da ake masa, daga nan aka tasa keyarsa zuwa magarkama har sai ya cika ka'idar beli

Jihar Legas - Wani Raymond Akala Ayodele mai shekaru 36 ya shiga hannun hukuma an kuma gurfanar dashi a gaban kotu bisa zargin ya karbi N3m na wata malamar makaranta mai zaune a Ikorodu a jihar Legas, Mrs Omowumi Arowosegbe.

Ayodele ya yi kirarin cewa, shine babban manajan ERIIFEi Divine Global Enterprise kuma fasto ne shi. Jami'an sashe na 2 na rundunar 'yan sandan jihar Legas sun damke shi, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro Sun Damke Mai Garkuwa da Mutane Yana Tsaka da Siyan Abinci a Kwara

A cewar 'yan sanda, Ayodele, wanda kuma ya yi ikrarin shi tsohon ma'aikacin Friesland Capena ne da ke Ogba a Legas, ana zargin ya karbi kudade daga matar da sunan zai yi kasuwanci da kudin kana su raba riba.

An ruwaito cewa, bayan da matar ta tura masa kudi a asusun banki, kawai aka nemi Ayodele aka rasa, inda ya cika wandonsa da iska tare da kudin.

An daure fasto saboda cin kudin malamar makaranta N3m
An Tasa Keyar Fasto Gidan Yari Bisa Zargin Damfarar Malamin Makaranta N3m | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fasto ya fece da kudin da yace zai yi kasuwa dasu

Bayan jin shuru, matar ta kai batun ga 'yan sanda ta hannun mataimakin sufeto janar na sashe na 2 a Legas, shi kuwa ya tura jami'ai su kwamuso malam fasto.

Tuni 'yan sanda suka yi himma, suka tabbatar da kamo Ayodele daga maboyarsa tare da damka shi ga magarkama.

An gurfanar dashi a gaban kotun Majistere ta Tinubu da ke tsibirin Legas bisa laifuka guda biyu da suka hada da karbar kudi ta hanyar sharara karya da kuma sata.

Kara karanta wannan

'Na Maka Magiya Dan Allah' Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Roki Wike Ya Goya Masa Baya a 2023

Dan sanda mai gabatar da kara SP Ibrahim Haruna ya shaidawa kotu cewa, mutumin ya aikata laifukan ne a cikin watan Fabrairun 2022, Within Nigeria.

Haruna ya shaidawa kotu cewa, Ayodele ya karbi kudade N3m daga malamar da sunan zai suba su a kasuwanci su raba riba, amma ya yi fecewarsa.

An ba da belin fasto bisa sharadi

Haruna ya kuma shadawa kotu cewa, laifukan da Ayodele ya aikata abin hukuntawa a karkashin kudin laifuka da hukunci na jihar Legas, sashe na 314(1) da 287, 2015.

Sai dai, wanda ake zargin ya musanta zargin da ake masa, mai shari'a Mrs Ggajumi Ayoku ta ba da belinsa a kan kudi N750,000 tare da kawo masu tsaya masa mutum biyu.

Ayoku ta kuma daga ci gaba da zaman sauraran karar zuwa ranar 7 ga watan Disamba, tare umartar a tsare Ayodele har sai ya cika ka'idar beli.

A wani labarin kuma, an kama ma'aikatan gwamnati, ciki har da wadanda suka yi ritaya bisa zargin sace kudin gwamnati.

Kara karanta wannan

Hoton ‘dan Najeriya Ya Kai $500k Banki Domin Adanawa ya Ba Jama’a Mamaki

Asali: Legit.ng

Online view pixel