Labari Mai Dadi: FG Ta Bayyana Lokacin da Jiragen Kasan Abuja-Kaduna Zasu Dawo Aiki

Labari Mai Dadi: FG Ta Bayyana Lokacin da Jiragen Kasan Abuja-Kaduna Zasu Dawo Aiki

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna zasu dawo da karakaina kafin makonni biyu masu zuwa
  • Ministan sufuri, Mu’azu Sambo ya sanar da hakan inda yace kafin watan Nuwamba ya kare jama’a zasu samu damar amfani da jiragen kasan
  • Ya jaddada cewa, tsaro zai inganta ga ‘yan Najeriya dake son amfani da jiragen kasan don gwamnati ta shirya tsaf wurin tsare rayukan ‘yan Najeriya

Gwamnatin tarayya tace jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna zasu dawo aiki kafin nan da makonni biyu, Daily Trust ta rahoto.

Minista Muazu Sambo
Labari Mai Dadi: FG Ta Bayyana Lokacin da Jiragen Kasan Abuja-Kaduna Zasu Dawo Aiki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ministan sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a filin jirgin kasa dake Moniya a Ibadan yayin da yaje ziyarar duba wurin karo na farko.

Za a ba jama’a tsaro

Ya tabbatarwa da fasinjojin jirgin kasa na fadin kasar nan cewa za su kasance masu matukar tsaro a yayin da suka hau jiragen kasan, jaridar Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tsohon Ministan Noma Tsaro, Shettima Mustapha Ya Kwanta Dama

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ministan da ya samu rakiyar karamin ministan sufuri, Prince Ademola Adegoroye, manajan daraktan hukumar kula da jiragen kasan, NRC, Fidet Okhiria da sauran jami’an ma’aikatar, yace gwamnatin tarayya ba zata sassauta ba wurin tabbatar da tsaro a jiragen kasan ba.

“Mun sanar a baya cewa za a cigaba da aiki a wannan titin dogon wannan watan. Muna da ranar da muke kallo.
“Ba dole bane in bayyana muku ranar, ina ganin hakan ba zai taimaki wadanda ke kula da harkar ba, ‘yan Najeriya dake bukatar amfani da jiragen, amma kafin nan da makonni biyu kuma kafin fitar watan nan, kawai ku kara hakuri.”

- Ya kara da cewa.

An ta yada cewa jiragen kasa zasu dawo aiki a watan Nuwamba

A cikin makonnin da suka gabata ne aka dinga yada cewa gwamnatin tarayya tace za a dawo da karakainar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

An Gurfanar da Mutum 16 ‘Yan Kasar Waje a Kotun Najeriya Saboda Zargin Satar Mai

Sai dai kwanaki kadan bayan fitar wannan labarin, gwamnatin tarayya ta fito tare da musantawa, lamarin da yasa murna ta koma ciki ga masu daukin komawa hawa jiragen kasan.

Farmakin jiragen kasa

A karshen watan Maris ne ‘yan ta’adda suka budewa jirgin kasa dauke da fasinjoji wuta inda suka sace jama’a tare da halaka wasu.

Sun tatsi kudin fansa daga iyalan fasinjojin amma basu halaka ko mutum daya ba cikin wadanda suka damke zuwa daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng