An Gurfanar da Mutum 16 ‘Yan Kasar Waje a Kotun Najeriya Saboda Zargin Satar Mai
- An cafke jirgin wasu ‘yan kasar waje ya shigo iyakar Najeriya ba tare da samun izinin hukuma ba
- Jirgin sojojin ruwa yana shawagi ne sai ya hangi wadannan mutane a cikin jirgin Mt. Heroic Idun
- Shari’a ta je gaban babban kotun tarayya na Fatakwal, kuma Alkali yayi umarni a tsare wadannan baki
Rivers - Babban kotun tarayya da ke zama a garin Fatakwal a jihar Ribas, ya gurfanar da mutane 16 ‘yan kasar waje da hannu wajen satar mai.
Rahoton The Guardian yace ana tuhumar wadannan mutane a gaban Mai shari’a Adamu Turaki Mohammed na babban kotun tarayya a Ribas.
Mutanen da ake tuhuma da laifi ‘yan kasashen Foland, Indiya, Sri-Lanka ne da kuma Fakistan wanda aka ga jirginsu ya tsalloka cikin Najeriya.
An gurfanar da su a gabban Adamu Turaki Mohammed dauke da jirgin ruwansu na Mt. Heroic Idun, kuma Alkalin ya bukaci a cigaba da tsare su.
Ana zarginsu da aikata laifuffukan ruwa wadanda sun ci karo da sashe na 10 da na 12 na dokar ruwa da makamantan laifuffuka ta shekarar 2019.
An ga jirgin Heroic Idun a wajen rijiyoyin mai
This Day tace ana karar wadannan Bayin Allah da shiga filin rijiyar man Akpo Oil da ke jihar Ribas, suna gujewa jirgin sojojin ruwan Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A laifuffukan da aka karanto masu, har da dillancin danyen man Najeriya, wanda wannan babban laifi ne a karkashin kundin tsarin mulki da doka.
Ba mu aikata laifi ba - Kyaftin
Duka mutane 16 da aka yi kara sun halarci zaman kotun da aka yi a farkon makon nan, har da shugaban jirgin ruwansum Kyaftin Mehta Tanuj.
Kyaftin Tanuj wanda mutumin Indiya ne, yace ba suyi laifi ba, umarnin manyansu ne suke bi.
Lauyoyi sun gabatar da bukatunsu
Lauyan da ya shigar da kara, Abidemi Adewumi-Aluko ya roki a dage shari’ar zuwa washegari domin a saurari abin da wadanda ake kara za su fada
Udoka Ezeobi wanda shi ne ya tsayawa wadanda ake jifa da laifi, bai kalubalanci bukatar Abidemi Adewumi-Aluko ba, yace a tsare su a jirgin na su.
Alkalin ya amince da bukatun lauyoyin, yace a tsare dukkaninsu a jirgin ruwansu tare da ba su damar ganin likita idan har bukatar hakan ta tashi.
Shari'ar zabe a Akwa Ibom
Rahoto ya zo an karbe takarar Gwamna aAkwa Ibom daga hannun Akanimo Udofia saboda bai dade da barin PDP ba, ya samu tikiti a Jam’iyyar APC.
Abokin neman takaransa watau Ita Enang ya ji dadin hukuncin da aka yi, amma Shugaban jam’iyya ya yi Allah-wadai da matakin da kotu ta dauka.
Asali: Legit.ng