Hukuma Ta Kama Ma’aikatan Gwamnati da Masu Ritaya Bisa Tafka Zambar N4.8bn

Hukuma Ta Kama Ma’aikatan Gwamnati da Masu Ritaya Bisa Tafka Zambar N4.8bn

  • Hukumar dakile cin hanci da rashawa ta kwamushe ma'aikata bisa zargin aikata zamba kan wani aiki
  • An kuma zargi wasu kamfanoni uku da hannu a lamarin, lamarin da ya kai ga fara bincike mai zurfi a kan lamarin
  • Kotu ta ba da umarnin kamo dan takarar sanata a jam'iyyar APC a jihar Kano bisa zargin ya damfari wani dan kasar waje

Jihar Oyo - Hukumar dakile cin hanci da rashawa ta jihar Oyo ta kama ma'aikatan gwamnati da wasu wadanda suka yi ritaya bisa zargin zamba a aikin kwangilar N4.8bn da aka bayar a 2018.

Shugabar hukumar, Mai shari'a Eni Esan (mai ritaya) ta bayyana a cikin wata sanarwa ta ranar Laraba cewa, wasu daidaiku ne suka yi cinye kudin a karkashin hukumar gyaran tituna ta jihar, kamar yadda hukumar ta gano a wasu bayanai da ke hannunta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hotunan Yadda Gobara Ta Laƙume Dukiyoyin 'Miliyoyi' A Kasuwar Singer Ta Kano

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ya zuwa yanzu hukumar na ci gaba da tattara bayanan da suka dace don kai maganar gaba, rahoton Punch.

An kama ma'aikatan gwamnati bisa cin kudin aiki N4.8bn
Hukuma Ta Kama Ma’aikatan Gwamnati da Masu Ritaya Bisa Tafka Zambar N4.8bn | Hoto: @seyiamakinde
Asali: UGC

An tura kudi ga wasu kamfanoni 3, amma basu yi aiki ba

Esan ta ce, zambar da ake zargi ta faru ne ta hanyar biyan wasu kamfanoni uku N4.8bn amma kuma basu yi aikin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yanzu haka hukumar na bin diddigin kamfanonin, hakazalika ana ci gaba da bincikar jami'an gwamnati da ke da hannu a cikin lamarin.

Hakazalika, hukumar ta nemi kamfanonin uku da su ba da bahasin kudaden da aka ce sun shiga asusun bankinsu tare da yin karin bayani.

A bangare guda, hukumar ta jaddada cewa, babu wanda yafi karfin doka, kuma tabbas doka za ta yi aiki akan wadanda ke da hannu a lamarin, Daily Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Jama’ar Ngala da N255m, Kayan Abinci da Sutturu

Ba sabon abu ne kudade su bata a hukumomin gwamnati, musamman a fannin ayyukan da suka shafi gine-gine.

Kotu ta umarci a kama dan takarar sanatan APC a jihar Kano, AA Zaura

A wani labarin kuma, kunji cewa, kotu a jihar Kano ta ba da umarnin a kamo AA Zaura don ci gaba da shari'ar da aka dashi kan damfara wani dan kasar waje.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, a baya an fara zama da Zaura kan lamarin, amma ya nemi daga karar zuwa kotun gaba, sai dai, kotu bata samu labari ba.

Mai shari'a ya ce a kotunsa za a ci gaba da zama tun bai samu bayani a rubuce na daga kara ba, kana ya umarci a kawo masa Zaura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel