Kotu Ta Umurci EFCC Ta Kamo Dan Takarar Sanatan Kano Na APC, AA Zaura

Kotu Ta Umurci EFCC Ta Kamo Dan Takarar Sanatan Kano Na APC, AA Zaura

  • Wata kotu a jihar Kano ta ba EFCC umarnin sake gurfanar da AA Zaura a gabanta bisa zargin damfarar wani dan kasar waje
  • A farko an wanke AA Zaura, amma kotu ta sake cewa a sake sauraran karar tare da binciko gaskiyar abin da ke faruwa
  • An kai ruwa rana a kotu, daga karshe alkali ya nemi a kamo Zaura, sannan a dawo a ci gaba da shari'a a ranar 5 ga watan Disamba

Jihar Kano - Kotun tarayya mai zama a jihar Kano ta umarci hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC da ta kamo Abdulkareem Abdulsalam Zaura, dan takarar takarar sanata na jam'iyyar APC a Kano ta tsakiya tare kawo shi gaban kotu.

Ana zargin AA Zaura ne da laifukan da suka shafi almundahana da damfara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wasu Sun Je Kotu Domin Hana Tinubu Shiga Zabe, Alkali Ya Fara Biya Masu Bukata

Mai shari'a Mohammed Nasiru Yunusa ne ya ba da wannan umarni a ranar Alhamis bayan da masu shigar da kara suka shaidawa kotu cewa, dan takarar na APC bai halarci zaman kotu ba a zaman da aka yi sau biyu.

An umarci EFCC ta sake kamo AA Zaura
Kotu ta umurci EFCC ta gurfanar da dan takarar Sanatan Kano na APC AA Zaura | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Farkon abin da ya faru

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahotanni sun ce, ana zargin AA Zaura ne da damfarar wani dan kasar Kuwait kudaden da suka kai $1.3m.

An sake gurfanar da Zaura ne a gaban kuliya bayan da kotun daukaka kara ta soke wanke shi da sallamarsa da wata kotu ta yi a baya, kana ta umarci a sake shari'ar.

Dalilin da yasa bai halarci zaman kotu ba

A zaman kotu na ranar Alhamis, lauyansa Ibrahim Waru ya shaidawa mai shari'a cewa, a yanzu kotun ba ta da hurumin sauraran karar, saboda tuni Zaura ya daukaka shari'ar da aka umarci a sake zuwa kotun koli, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Wani Alkalin kotu Ya ci Na Jaki a Hannun Wasu Ma'aikata a Jihar Kebi

Sai dai, mai shari'a ya ce, kotunsa na da hurumin sauraran shari'ar, saboda bai samu rubutacciyar takarda da ke nuna Zaura ya daukaka kara ba.

Bayan umarnin kotu na dauko Zaura, lauyan EFCC, barista AI Aroghn ya ce hukumar za ta yi duk mai yiwuwa domin kamo shi tare da gurfanar dashi a gaban kotun.

Daga nan ne aka daga sake sauraran karar zuwa ranar 5 ga watan Disamban 2022 ga mai rai.

A wani labarin, bayan da kotu ta umarci a kama shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa, wani lauya ya shawarce shi da ya gaggauta mika kansa.

An zargi Bawa ne da kin bin umarnin kotu na mayar da wasu kayayyaki da aka kwace a hannun wanda ake zargi da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel