Zaben 2023: Ni Fa Na Riga Na Tare A Abuja, Tinubu Ya Fada Wa Atiku

Zaben 2023: Ni Fa Na Riga Na Tare A Abuja, Tinubu Ya Fada Wa Atiku

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya ce ya baro gidansa na Legas ya tare a Abuja
  • Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tattaunawa da takwararsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da suka hadu a filin tashin jiragen sama na Abuja
  • Bidiyon yan takarar shugaban kasar biyu wanda ke neman gadon kujerar Shugaba Muhammadu Buhari ya bazu a kafafen watsa labarai

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya tare a Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Tinubu, jigon siyasan jihar Legas, yana zaune ne a Bourdillon drive a unguwar Ikoyi a birnin Legas.

Atiku da Tinubu
2023: Ni Fa Na Riga Na Tare A Abuja, Tinubu Ya Fada Wa Atiku. Hoto: @APCPresCC2022
Asali: Twitter

Wanda ake yi wa lakabi da zaki na Bourdillon, manyan yan siyasa su kan ziyarci gidansa na Legas domin neman shawara kan harkokin siyasa, da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Kicibus: Bidiyon yadda Tinubu da Atiku suka yi gamuwar ba zata a filin jirgin sama

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma a lokacin da ya hadu da takwararsa na jam'iyyar Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a filin tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe a Abuja, a ranar Litinin, Tinubu ya ce yanzu ya tare a babban tarayyar Najeriya.

Atiku ya tambaya:

"Za ka tafi Legas ne?."

Da ya ke bada amsa, Tinubu ya ce:

"Na koma Abuja da zama".

Duk da banbancinsu na siyasa musamman a yanzu da kamfen ya fara daukan zafi, mutanen biyu sun rika murmushi da juna yayin da suke gaisawa tare da mukarrabansu a gefe guda.

Takaitaccen tarihin alakar siyasar da ke tsakanin Tinubu da Atiku

Atiku da Tinubu suna da tsohuwar alaka ta siyasa. Yayin da Tinubu ke gwamna a jihar Legas daga 1999 zuwa 2007, Atiku ne mataimakin shugaban kasa.

Atiku, wanda ya samu matsala da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a kokarinsa na gaje gujerarsa, daga bisani ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Congress (AC), jam'iyyar da Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wurin kafa ta bayan gwamnonin jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) da aka zaba a 1999 sun fuskanci 'babban kaye'.

Kara karanta wannan

Rashawa: Atiku waliyyi ne a kan irinsu Tinubu da Obi, jigon PDP ya fadi karamomin Atiku

Mutanen biyu duk suna cikin wadanda aka kafa jam'iyyar APC mai mulki a kasa da su, inda Atiku ya yi takarar tikitin shugaban kasa a 2014 amma ya zo na uku bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a yanzu shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Shugaba Muhammadu Buhari ya samu tikitin kuma daga bisani ya yi nasara a babban zaben 2015 ya kafa tarihi a matsayin lokaci na farko da jam'iyyar hamayya ta mulki Najeriya. Buhari ya kada tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda a lokacin ya ke neman yin tazarce.

Bidiyon Yadda Atiku Ya Gamu da Tinubu a Filin Jirgin Saman Abuja, Sun Yi Raha

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya hadu da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a filin jirgin sama a Abuja.

A wani bidiyon da tawagar kamfen na jam'iyyar APC ta yada a kafar Twitter, an ga lokacin da 'yan takarar biyu ke zaune suna raha a wani wuri mai kama da dakin jira na tashar jirgin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164