Bidiyon Yadda Atiku Ya Gamu da Tinubu a Filin Jirgin Saman Abuja, Sun Yi Raha

Bidiyon Yadda Atiku Ya Gamu da Tinubu a Filin Jirgin Saman Abuja, Sun Yi Raha

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya gamu da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar
  • Sun gamu ne a filin jirgin saman Abuja yayin da kowa ke kan harkarsa ta batun gangamin kamfen a jihohin kasar nan
  • 'Yan siyasa a Najeriya na ci gaba da musayar maganganu don nuna 'yan takararsu ne suka cancanci gaje Buhari a 2023

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya yi kicibus da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a filin jirgi a babban birnin tarayya Abuja

A wani bidiyon da tawagar kamfen na jam'iyyar APC ta yada a kafar Twitter, an ga lokacin da 'yan takarar biyu ke zaune suna raha a wani wuri mai kama da dakin jira na tashar jirgin.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyoyi Sun Yi Gangami a Wata Jihar Arewa, Sun Yi Alkawarin Kawowa Tinubu Kuri'u Miliyan 4

A cewar tawagar APC, dan takararsu; Tinubu na kan hanyarsa ta zuwa birnin Jos na jihar Filato ne domin kaddamar da kamfen dinsa a can.

Shi kuwa Atiku, an ce yana kan hanyarsa ta dawowa gida ne daga wan gangamin kamfen da ya halarta.

Tinubu ya gana da Atiku
Bidiyon Yadda Atiku Ya Gamu da Tinubu a Filin Jirgin Saman Abuja, Sun Yi Raha | Hoto: @APCPresCC2022
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayani daga tawagar kamfen na APC

Bidiyon da tawagar kamfen ta APC ta yada na dauke da rubutun da ke cewa:

"Asiwaju Bola Tinubu ya hadu da Atiku a sashen jirage masu zaman kansu na filin jirgin Nnamdi Azikwe.
"Asiwaju na nufi Jos ne gabanin kaddamar da gangamin kamfen dinsa yayin da Atiku kuwa ya dawo daga wani gangamin kamfen."

An ga Atiku da Tinubu suna tattaunawa cikin raha, tare da nuna alamar abota da aminci a tsakaninsu.

Jam'iyyun siyasa na ci gaba da tallata 'yan takarsu gabanin zaben 2023 mai zuwa, tare da musayar kalamai a tsakanin juna.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Sai dai, har yanzu abin da ke kara daukar hankalin jama'a shine, yadda 'yan takarar idan suka gamu ba sa nuna alamar adawa da juna.

Kalli bidiyon ganawarsu:

Atiku ba dan rashawa bane, ba ya kuma siyar da kwaya, inji jigon PDP

A wani labarin kuma, jigon jam'iyyar PDP ya caccaki 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun APC da Labour yayin da ake ci gaba da gangamin kamfen zaben 2023.

Reno Omokri ya tono batutuwan da suka shafi Tinubu da Peter Obi, ya ce Atiku yana da tsafta idan aka kwatanta shi dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel