'Yan Bindiga Sun Sace Wani Limamin Katolika Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna

'Yan Bindiga Sun Sace Wani Limamin Katolika Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna

  • Rahotannin da ke fitowa daga jihar Kaduna sun bayyana cewa, wasu tsagerun 'yan bindiga sun farmaki wani fasto, sun tafi dashi
  • Hakazalika, an sace wata mata da 'ya'yanta yayin da wasu 'yan bindigan suka kutsa har gida suka aikata barna
  • Majiyoyi sun tabbatar da faruwar lamarin, amma ba a samu jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kaduna ba.

Jihar Kaduna - 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wani malamin cocin garin Idom, Reverend Father Abraham a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Daily Trust ta tattaro cewa, an yi awon gaba da wannan malamin ne a garinsu mai suna Kurmin Sara da ke karamar hukumar ta Kachia.

Ya zuwa yanzu dai babu wasu bayanai cikakku na yadda aka sace, amma majiyoyi da dama a jihar sun tabbatar da an sace malamin.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Hargitsa Kauye, Sun Yi Awon Gaba da Basarake da Mutanen Gari

Shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, Reverend Joseph Hayeb ya tabbatar da sace faston ga majiya.

'Yan bindiga sun sace babban limamin katolika a Kaduna
'Yan Bindiga Sun Sace Wani Limamin Katolika Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna | Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

“Lamari ne da ko kadan bai yi dadi ba saboda shine malami a garin Idon amma kasa sace shi a kauyen Kurmin Sara a karamar hukumar Kachia.
“Abun babu dadi saboda abubuwa da dama na faruwa mamma ba yin rahoton abin da ke faruwa ba."

Ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar yin abubuwa masu yawa da suka dace don kare mazauna yankin daga barnar ‘yan ta’adda.

An sace wata mata a Kaduna

Hakazalika, rahoton This Day ya ruwaito cewa, 'yan bindigan sun kutsa wani gida inda suka sace wata mata da mijinta ya rasu.

Majiya ta ce, matar ta fita kasuwa siyayya, kwatsam da ta dawo sai ta ji alamar motsi a cikin, lamarin da ya sanya mata kokwanto.

Kara karanta wannan

Za mu zama marasa amfani idan muka bari Tinubu yaci zabe, Kiristocin Arewa

An ce daga nan ne 'yan ta'addan suka yi awon gaba da ita da wasu 'ya'yanta a daidai lokacin da ta shigo gidan.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ba, Muhammad Jalige.

An sako 'yan mata 5 na tsohon akanta da aka sace a Zamfara

Wani rahotonmu na baya ya bayyana yadda wasu 'yan bindiga suka sako 'yan mata biyar da suka sace a gidan tsohon akanta-janar na jihar Zamfara.

A baya tsagerun sun yi barazanar mai da 'yan matan cikinsu, inda suka dauki makamai suka ba su a wani bidiyo.

Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar hare-haren 'yan bindiga a 'yan shekarun nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel