Masu Garkuwa Sun Fada Komar Yan Sanda Yayin Da Suke Kokarin Karbar Cikon Kudin Fansa A Wata Jihar Arewa

Masu Garkuwa Sun Fada Komar Yan Sanda Yayin Da Suke Kokarin Karbar Cikon Kudin Fansa A Wata Jihar Arewa

  • Yan sanda daga Jihar Gombe sun yi nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane a Kano yayin da suke yunkurin N300,000 na fansa
  • Mahid Abubakar, kakakin yan sandan Gombe ya ce hakan na zuwa ne bayan wadanda ake zargin sun fara karbar N100,000 daga iyalan wanda suka sace
  • Abubakar ya ce wanda ake zargin ya bayyana cewa shi da wani Saidu Salisu da Turkani ne suka sace Jibrin Muhammad na kauyen Bantaje a Taraba

Gombe - Rundunar yan sandan Jihar Gombe a ranar Talata ta yi holen wani Mohammed Aminu da Salisu Sa'idu, wadanda aka kama yayin karban kudin fansa N300,000 daga iyalan wadanda suka sace.

A cewar kakakin rundunar, Mahid Abubakar, hakan na zuwa ne bayan tawagar masu garkuwar sun karbi N100,000 bayan sace wani Jibrin Muhammad a Jihar Taraba, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Mabaraci Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayinda Aka Kamashi Kudi N500,000 a jihar Legas

Taswirar Jihar Gombe
Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Yayin Karbar Kudin Fansa A Wata Jihar Arewa. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa tawagar binciken manyan laifuka, SCID ne ta kama Sa'idu a Kano yayin bincike.

Abubakar ta ce:

"Yan sanda na sashin X-squad SCID a Gombe, bayan samun bayanan sirri ta kama wani Mohammed Aminu na Tudun Wada Quaters a Gombe a lokacin da suke kokarin kudin fansa dubu dari uku (N300,000) bayan an biya su N100,000 a wani asusun bankin Ja'iz mai suna Mohammed Al'amin Muhammad.
"A yayin bincike wanda ake zargin ya ce shi da wani Saidu Salisu da aka fi sani da Soja da Turkani sun hada baki samu bindigu AK-47 kuma sun sace wani Jibrin Muhammad na kauyen Bantaje a karamar hukumar Wukari kuma sun kari N400,000 matsayin kudin fansa.
"Da ake bincike, jami'an yan sanda na SCID Gombe sun kama wani Salisu Sa'idu a Kano. Ana cigaba da bincike idan an kammala za a gurfanar da su a kotu."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

Abubakar ya bukaci mazauna jihar su rika tallafawa rundunar da bayanai masu amfani domin kawo karshen laifuka, yana mai cewa za a sirrinta sunayensu.

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel