‘Yan Sanda Sun Dakile Farmakin da ISWAP ta Kai Caji Ofis a Magumeri, Borno

‘Yan Sanda Sun Dakile Farmakin da ISWAP ta Kai Caji Ofis a Magumeri, Borno

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da dakile wani harin ‘yan ta’adda wanda mayakan ISWAP suka kai caji ofis din Magumeri
  • ‘Yan ta’addan sun tsinkayi caji ofis din wurin karfe 12:35 na safiyar Lahadi a motocin yaki da babura, sun harbi sifetan ‘dan sanda daya
  • Dakarun sojin Najeriya sun halaka ‘yan Boko Haram uku dake wa matafiya fashi a titin Gubio inda suka samo AK47 biyu, babur da harsasai

Borno- Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta dakile wani farmaki da wasu da ake zargin mambobin ISWAP ne suka kai a birnin Magumeri dake jihar.

Borno Police
‘Yan Sanda Sun Dakile Farmakin da ISWAP ta Kai Caji Ofis a Magumeri, Borno. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda Zagazola Makama, wata wallafa da ta mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi ta bayyana, wadanda ake zargin mayakan ISWAP ne suka tsinkayi caji ofis din ‘yan sanda dake garin a tawagar motocin yaki da babura wurin karfe 12:35 na safiyar lahadi.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun yi wa Basarake Yankan Rago a Najeriya

Wata majiya makusanciya da wadanda suka dakile harin tace harin yayi sanadin musayar ruwan wuta tsakanin jami’an ‘yan sandan da ‘yan ta’addan.

Makama ta kara da tattaro cewa, yayin da tawagar ‘yan sandan suka iya dakile farmakin cike da nasara, an harba wani Bitrus Umaru, ‘dan sanda mai mukamin Sifeta, a ciki da kafarsa ta dama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Yan ta’addan sun yi awon gaba da wata mota kirar Hilux ta sintiri.

Soji Sun Halaka ‘Yan Boko Haram 3

A daya bangaren kuwa, dakarun rundunar Operation Hadin Kai dake karkashin rundunar sojin kasan Najeriya ta halaka ‘yan Boko Haram uku a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno.

Kamar yadda Makama suka bayyana, dakarun sojin sun halaka su sakamakon musayar ruwan wuta da suka yi da ‘yan ta’addan.

Wallafar ta kara da cewa, dakarun tare da hadin guiwar jami’an CJTF sun cafke wasu ‘yan ta’addan dake fashi ga matafiya a yammacin Juma’a.

Kara karanta wannan

Niger: ‘Yan Ta’adda Sun Halaka Mafarauta 5, Sun Yi Garkuwa da Fasinjoji Babu Adadi

Wata majiya ta sanar da Makama cewa biyu daga cikin ‘yan ta’addan suna dauke da bindiga kirar AK47 yayin da na uku ke kan babur.

“Mun samo bindigogi kirar AK47 guda biyu, harsasai da babur daga ‘yan ta’addan.”

- Majiyar tace.

Niger: ‘Yan Ta’adda Sun Halaka Mafarauta 5, Sun Yi Garkuwa da Fasinjoji Babu Adadi

A wani labari na daban, Matafiya masu tarin yawa da ba a san adadinsu ba har yanzu da suka nufi Kontagora an yi garkuwa da su yayin da ‘yan ta’adda suka halaka mafarauta biyar a kusa da Garin Gabas dake karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, ‘yan ta’addan sun bayyana a sama da babura 40 inda suka rufe titin tare da tsayar da masu ababen hawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel