Soyayya Ta Gaskiya: Bidiyon Yadda Ango Ya Goyo Amaryarsa A Babur Zuwa Wajen Daurin Aurensu Ya Ja Hankali

Soyayya Ta Gaskiya: Bidiyon Yadda Ango Ya Goyo Amaryarsa A Babur Zuwa Wajen Daurin Aurensu Ya Ja Hankali

  • Wani hadadden matashiya wanda ya goya amaryarsa a kan babur dinsa a ranar aurensu ya sha ruwan yabo a soahiyal midiya
  • A wani bidiyo da ke yawo a TikTok, an gano mutumin a kan babur tare da amaryarsa da babbar kawar amarya
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun jinjinawa masoyan da basu ari rayuwar karya sun yafa ba, maimakon haka suke farin ciki da abun da suke da shi

Jama'a sun yi cece-kuce bayan ganin bidiyon wani matashi wanda ya goyo amaryarsa a babur a ranar aurensu.

A wani bidiyo da @Mujunimedardmujuni ya wallafa a TikTok, mutumin ya tuka babur din tare da amaryarsa da babbar kawarta yana mai alfahari da abun da Allah ya raba ya bashi.

Mutane a kan babur
Soyayya Ta Gaskiya: Bidiyon Yadda Ango Ya Goyo Amaryarsa A Babur Zuwa Wajen Daurin Aurensu Ya Ja Hankali Hoto: TikTok/@mujunimedardmujuni.
Asali: UGC

Alamu sun nuna amarya da angon na a hanyarsu ta zuwa wajen daurin aurenau ne. Matar ta yane kanta da mayafi yayin da mijin ya sanya kwat da wando.

Kara karanta wannan

"Dole Mahaifiyarta Ta Zama Lakcara" : Saurayi Ya Lissafa Abubuwan Ya Ke Bukata Daga Matar Da Ke Son Aurensa A Najeriya

Sai dai kuma, ba a tabbatar da ko mijin dan achaba bane ko kuma kawai matar ta yanke shawarar zuwa wajen auren nasu kan babur ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidoyon a kasa:

Masu amfani da TikTok sun aike masu da sakonni na taya murna

@patmore 77 ta ce:

"Na fada tarkon son motar ta musamman. Allah ya albarkaci aurenku."

cissy Akky ya yi martani:

"Wannan shi muke kira da soyayya ta gaskiya da manyan harufa."

@kansi44 ya ce:

"Babu wanda zai iya samar da mota don jigila. Ina tayaku murnar aure."

@user8867290433852 ya ce:

“Wow Allah ya baku tsawon rai da rayuwar aure mai cike da farin ciki.”

Bidiyo: Matashiya Yar Shekaru 40 Ta Koka Saboda Rashin Mijin Aure, Ta Roki Allah Ya Kawo Mata Agaji

A wani labarin, wata matashiyar budurwa mai shekaru 40 ta koka kan cewa bata jin dadin yadda abubuwa ke tafiya a rayuwarta. Da take wallafa bidiyo a TikTok cike da rudani, budurwar ta rubuta cewa bata da haihuwa ko miji.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shigar Ango Wurin Shagalin Aurensa a Akwatin Gawa Ya Gigita Amarya

Budurwar ta kara da cewa bata da wani tsayayyen namiji a yanzu haka sannan ta roki Allah da ya kawo mata dauki.

"Shekaruna 40 yanzu, ba da, ba miji, babu wani tsayayye da muke soyayya a yanzu haka. Ya Allah ka taimake ni," ta rubuta a bidiyon mai taba zuciya. "

Asali: Legit.ng

Online view pixel