Bidiyon Ango Ya Bayyana Wurin Shagalin Bikinsa a Akwatin Gawa

Bidiyon Ango Ya Bayyana Wurin Shagalin Bikinsa a Akwatin Gawa

  • Wani mutumi ya bayyana bidiyon yadda wani ango yayi shigar bada mamaki wurin aurensa inda ya bayyana a cikin akwatin gawa
  • Amaryar ta bayyana cike da mamaki yayin da ta ga akwatin gawar dake dauke da rayayyen angonta ya shigo cikin wurin daurin aurensu
  • Jama’a da suka kalla bidiyon sabon salon na angon sun ce komai ya baci kuma wannan salon bai yi ba don yafi kama da bikin mutuwa

Wani gajeren bidiyo da @tobz88 ya wallafa ya nuna lokacin da wani mutum ya bayyana a wurin daurin aurensa a cikin akwatin gawa.

Ango a Akwatin gawa
Bidiyon Ango Ya Bayyana Wurin Shagalin Bikinsa a Akwatin Gawa. Hoto daga TikTok/@tobz88
Asali: UGC

Yayin da ‘yan biki da kyakyawar amaryarsa suka tsaya jiran ganin ango da tawagar abokansa, sun bayyana tamkar masu daukar akwatin gawa inda suka shigo da angon.

Ango ya bayyana a akwatin gawa

Kara karanta wannan

Mutane Na Cigaba da Fito da Kudin da Suka Boye, An Gano N200 da Aka Buga Tun 2003

A wani bidiyo da ya yadu a dandalin sada zumunta na TikTok, bayan an sauke akwatin gawan a bayan amaryar, sun bude shi kuma mutumin ya fito a cikin natsuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shagalin auren wanda aka yi shi a gabar ruwa, ya samu halartar baki wadanda suka dinga nadar abinda ke faruwa da wayoyinsu.

Jama’a sun yi martani

Mutane da yawa da suka yi martani kan bidiyon sun kwatanta wannan auren da irin wanda ba a saba gani ba.

Wasu sun ce ba zasu zauna a irin wannan auren ba balle a yi wani shagali dasu.

Kalla bidiyon a kasa:

A lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya samu jinjina sama da 600,000 da kuma tsokaci sama da 10,000.

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin tsokacin jama’a.

Gotham n Pawz yace:

“Na so ganin cewa wannan bikin mutuwa ne amma ba hakan ake yin shi ba ai.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Magidancin da ya Rangadawa Matarsa Mai Tsohon Ciki Tsulelen Kitso ya Birge Jama’a

Megan Urby yace:

“Ka fada min baka son yin auren kawai ba tare da ka furta ba.”

Christine Francesca yace:

“Dukkansu abun ya basu kunya. Ko ni ce zan tozarta da wannan abu gaskiya.”

DisMiss tace:

“Idan ni ce zan ce wannan rashin sa’a ce kuma take son bayyana a fili. A gaskiya ba zan lamunci irin wannan shigowa ba.”

Bee Rock yace:

“A kalla dai gashi yanzu a TikTok, don haka sama da mutum 12 suke ganin shi.”

Farin Barneycastle yace:

“Bayanin shi a nan shi ne, a farko rayuwa bata da amfani har sai da ya hadu da ita.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel