"Dole Mahaifiyarta Ta Zama Lakcara" : Saurayi Ya Lissafa Abubuwan Ya Ke Bukata Daga Matar Da Ke Son Aurensa

"Dole Mahaifiyarta Ta Zama Lakcara" : Saurayi Ya Lissafa Abubuwan Ya Ke Bukata Daga Matar Da Ke Son Aurensa

  • Wani dan Najeriya ya tafi shafinsa na Facebook ya lissafa abubuwan da ya ke bukata a macen da ke son aurensa
  • Mutumin mai suna Solomon Hangega ya wallafa rubutun ne a wani shafi mai suna Ukum Sons anda Daughters Connect Worldwide
  • Daya daga cikin abubuwa masu ban mamaki cikin jerin abubuwan da ya lissafa shine mahaifiyar matar da ke son aurensa ta kasance ma'aikaciyar jinya ko lakcara

Facebook - Solomon Hangega, wani dan Najeriya ya ce duk macen da ke son aurensa sai ta cika wasu ka'idoji da ya jera a rubutun da ya yi a Facebook.

A wani rubutu da ya yi a shafin 'Ukum Sons anda Daughters Connect Worldwide' a Facebook, Solomon Hangega ya ce dole mahaifiyar matar da zai aura ta kasance lakcara a Jami'a.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

Matashi mai neman aure
"Dole Mahaifiyarta Ta Zama Lakcara" : Saurayi Ya Lissafa Abubuwan Ya Ke Bukata Daga Matar Da Ke Son Aurensa. Hoto: Solomon Hangega.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan kuma mahaifiyar yarinyar ba lakcara bane, dole ta zama ma'aikaciyar jinya a sanannen asibiti.

Ga abin da Solomon ya rubuta:

"Matar da na ke son aure dole ta zama tana da halaye da ake bukata a matar aure. Dole ta fito daga Logo/Ukum/Gboko/Kwande
"A kalla tana da difiloma a bangaren kiwon lafiya ko digiri a kowanne sashi amma banda shari'a da watsa labarai. Dole mahaifinta ya zama dan siyasa kuma mai kudi, mahaifiyarta kuma dole ta zama ma'aikaciyar jinya ko lakcara a jami'a."

Mutane 150 sun tura bukatarsu a yanzu, in ji Solomon

A wani rubutun mai biye wa na farkon, duk dai a shafin, Solomon ya bayyana cewa fiye da mata 150 sun tura masa takardar nuna sha'awa a Facebook. Ya soki wadanda ke zaginsa a intanet.

Martanin wasu masu amfani da intanet

Kara karanta wannan

Bayan shiga daga ciki, ango ya yi wani gargadi mai zafi ga dukkan abokansa

A bangare guda, mutane a dandalin sada zumunta sun rika martani kan rubutun da ya yi na farko.

Duba wasu abubuwan da wasu cikinsu ke cewa:

Labisit Shittu ya ce:

"Kimiyyar dabobi wannan ke karantawa fa."

Terwase Anastencia ta ce:

"Hahaha. Zan shirya don in auri yar ka."

Doowuese Mlanga David ya ce:

"Ka ba su babu sasautawa. Tashin hankali muke so."

"Dole Ta Iya Larabci": Wani Dan Najeriya Ya Lissafo Sharrudan Da Matar Da Ke Son Auren Shi Za Ta Cika

A wani labarin mai kama da wannan, mutane sun yi ta tofa albarkacin bakinsu game da jerin sharruda na musamman da wani dan Najeriya wanda ke son aure ya lissafa.

A jerin sharrudan da ya wallafa a ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba, mai amfani da Twittan mai suna Banjo Hanjo ya ce dan uwansa na neman matan aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel