Sojoji da 'Yan Sanda Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Bayan Musayar Wuta a Anambra

Sojoji da 'Yan Sanda Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Bayan Musayar Wuta a Anambra

  • Gamayyar jami'an tsaro na hukumar soji da yan sanda sun halaka wasu tsagerun yan bindiga uku a jihar Anambra ranar Laraba
  • Bayanai sun nuna cewa bayan tura su barzahu, an gano layu a dukkanin sassan jikinsu da ya haɗa da kafa, hannu, wuya da sauransu
  • Duk da ba'a samu jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sanda ba, wani babban jami'i ya tabbatar da aukuwar lamarin

Anambra - Jami'an tsaro a jihar Anambra, kudu maso gabashin Najeriya, sun sheƙe wasu 'yan bindiga yayin wata kazamar musayar wuta a tsakaninsu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a ranar Laraba a ƙauyen Umunze da ke yankin ƙaramar hukumar, Orumba ta kudu a jihar.

Dakaru sun kashe yan bindiga uku a Anambra.
Sojoji da 'Yan Sanda Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Bayan Musayar Wuta a Anambra Hoto: thenationonlineng
Asali: UGC

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa 'yan bindiga sun sanya Layu a wurare daban-dabam na jikinsu wanda ya haɗa da kafafuwa, wuya, ƙugu da kuma hannuwa.

Kara karanta wannan

Kano: Alkali Ya Aike ‘Yan TikTok 2 Kurkuku Kan Zagin Ganduje da Bata Masa Suna

Haka nan kuma rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan da jami'ai suka tura barzahun mambobi ne a ƙungiyar da ta addabi mutanen yankin Orumba da ta'addaci kala daban-daban.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Anambra, Ikenga Tochukwu, domin jin ta bakinsa kan abinda ya faru ba'a same shi ba, domin wayarsa ta salula na kashe.

Amma ɗaya daga cikin manyan jami'an yan sanda a hedkwatar hukumar ya tabbatar da samun wannan nasarar ga jaridar The Nation.

Yace gamayyar dakarun 'yan sanda da sojoji ne suka aiwatar da Operation din da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin yau Laraba, 2 ga watan Nuwamba, 2022, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Jihar Anambra na ɗaya daga cikin jihohin dake fama da hare-haren yan bindiga waɗanda ake kyautata zaton yan haramtacciyar ƙunguyar 'yan aware ne wato IPOB.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun gamu da ajali, jami'an tsaro sun ragargaje su a wata jiha

Yan ta'adda sun kwashi kashinsu a hannu a Borno

A wani labarin kuma Sojin Najeriya Sun Halaka Sama da ‘Yan Ta’adda 15, An Rasa Sojoji 2 a jihar Borno

Dakarun sojin Najeriya tare da hadin kan ‘yan Sa kai na farar hula sun halaka ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP 15 a garin Banki dake Bama.

An gano cewa, sojojin sun yi dirar ba-zata a maboyar ‘yan ta’addan dake kauyen Gauri inda suke boye dabbobin sata da shirya harar sojin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel