Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga Uku a Jihar Anambra

Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga Uku a Jihar Anambra

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun gamu da ajalinsu yayin da suka yi arangama da jami'an tsaro a jihar Anambra
  • An ragargaji da dama, an kashe uku daga cikinsu, kamar yadda wani babban jami'i ya shaidawa majiyarmu
  • 'Yan bindiga sun addabi yankuna da dama a Najeriya, suna aikata munanan ayyukan ta'addanci

Jihar Anambra - Hadin gwiwar jami'an tsaro a jihar Anambra sun yi bata-kashi da wasu tsagerun 'yan bindiga, sun hallaka uku.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba a Umunze, karamar hukumar Orumba ta Kudu a jihar ta Anambra.

Rahoton da muke samo daga jaridar The Nation ya bayyana cewa, an samu layu da guraye a jikinsu, musamman a kafa, wuya, kugu da hannaye.

An tattaro cewa, 'yan bindigan na cikin tsagerun da suka addabi mazauna yankin Orumba da kai munanan hare-hare a 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Sojoji da 'Yan Sanda Sun Sheƙe Hatsabiban Yan Bindiga Uku, An Gano Wani Abu a Jikinsu

Ya zuwa yanzu dai ba a iya samun jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu ba.

Amma wani babban jami'i na hukumar ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa, hadin gwiwar jami'an 'yan sanda da sojoji ne suka gudanar da aikin a yau 2 ga watan Nuwamba da misalin karfe 4:30 na yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel