Kano: Alkali Ya Aike ‘Yan TikTok 2 Kurkuku Kan Zagin Ganduje da Bata Masa Suna

Kano: Alkali Ya Aike ‘Yan TikTok 2 Kurkuku Kan Zagin Ganduje da Bata Masa Suna

  • Alkali ya aike fitattun masu bidiyoyin barkwanci a TikTok, Mubarak Uniquepikin da Nazifi Muhammad gidan kurkuku a jihar Kano
  • Ana zarginsu da bata Gwamna Ganduje sun ta hanyar yin bidiyo dake bayyana shi matsayin ‘dan siyasa mai bakin cin rashawa
  • Bayan gurfanar da matasan, an karanto musu laifukan da ake zarginsu da su kuma sun amsa, lamarin da yasa alkali yace a kai su gidan maza kafin ya yanke hukunci

Kano - Wasu ma’abota amfani da TikTok wurin yin bidiyoyin bada dariya, Mubarak Muhammad wanda ka fi sani da Uniquepikin da Nazifi Muhammad an aikesu kurkuku kan zargin su da ake yi da bata sunan Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a daya daga cikin bidiyoyinsu.

TikToker
Kano: Alkali Ya Aike ‘Yan TikTok 2 Kurkuku Kan Zagin Ganduje da Bata Masa Suna. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Daily Nigerian ta tattaro cewa, masu bidiyon barkwancin sun yi bidiyo dake bayyana Ganduje matsayin ‘dan siyasa mai cin rashawa wanda ke siyar da duk wani fuloti na gwamnati da ya gani a jihar.

Kara karanta wannan

2023: Dan Allah Ku Yafe Mun Kura-Kuran Da Na Yi A Mulkina, Gwamnan Arewa Ya Roki Mutanen Jiharsa

Jami’an ‘yan sanda suka gurfanar dasu a gaban kotun majistare mai lamba 58 ta Nomansland wacce ke karkashin jagorancin alkali Aminu Gabari.

A yayin da aka karanto abubuwan da ake zarginsu da shi, masu TikTok din sun amsa laifinsu na hada kai tare da bata sunan gwamnan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A don haka alkalin ya bukaci da a adana su a gidan maza inda ya dage shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci.

Tuni jami’an tsaro suka tasa keyarsu.

'Yar TikTok Ta Sauke Jiji da Kai, Ta Nuna Sana’ar da Mahaifiyarta Ke Yi, Tana Taya Ta Aiki

A wani labari na daban, 'yan TikTok sun yiwa wata 'yar Najeriya mai kaudi a intanet tofin albarka saboda yadda take taimakawa mahaifiyarta.

A wani bidiyo da ta yada a asusunta na TikTok mai suna @brownsugarnice, ta shawarci 'yan mata masu kwalisa su ke taimakawa iyayensu.

Kara karanta wannan

Wata Fatima Abubakar Ta Zuba Wa Mijinta Guba a Abinci, Tace Ta Tsani Aure a Rayuwarta

Kasancewarta 'Slay Queen', hakan bai hana ta ayyukan gida, kuma takan yi amfani da lokacinta yadda ya dace.

Ta kuma yada wani hoto na lokacin da ta kammala ayyukanta, sannan ta fita waje domin shakatawa.

A wani sashe na biyu na hoton, an ganta a tsaye a wani gidan cin abinci, inda ta shakatawa bayan gama aikinta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel