Borno: Sojin Najeriya Sun Halaka Sama da ‘Yan Ta’adda 15, An Rasa Sojoji 2

Borno: Sojin Najeriya Sun Halaka Sama da ‘Yan Ta’adda 15, An Rasa Sojoji 2

  • Dakarun sojin Najeriya tare da hadin kan ‘yan da kai na farar hula sun halaka ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP 15 a garin Banki dake Bama
  • An gano cewa, sojojin sun yi dirar ba-zata a maboyar ‘yan ta’addan dake kauyen Gauri inda suke boye dabbobin sata da shirya harar sojin
  • Bayan halaka wasu, ‘yan ta’addan sun tsere inda suka gayyato ‘yan uwansu tare da kokarin far wa sojojin, sai dai hakan yasa sun kara rashin wasu 7

Borno - Dakarun sojin Najeriya sun halaka wasu mayakan ISWAP da Boko Haram sakamakon mummunan arangamar da suka yi a yankin Banki dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Dakarun Soji
Borno: Sojin Najeriya Sun Halaka Sama da ‘Yan Ta’adda 15, An Rasa Sojoji 2. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mayakan Boko Haram din sun gamu da ajalinsu ne yayin da dakarun bataliya ta 151 tare da hadin guiwar ‘yan da kai dake hade da rundunar Operation Hadin Kai suka dira maboyarsu dake kauyen Gauri a ranar 30 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun farmaki barikin soja, sojoji sun yi musu kaca-kaca a wata jihar Arewa

Wata majiyar sirri ta sanar da Zagazola Makama cewa dakarun sun tare sannan suka halaka wasu ‘yan ta’addan Boko Haram din dake kauyen.

Majiyar tace dajin ya kasance maboyarsu kuma a nan suke shirya duk wasu miyagun farmakin da suke kai wa sojoji sannan wasu ‘yan ta’addan suna amfani da wurin don boye dabbobin sata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayi bayanin cewa dakarun dake sintirin sun yi dabara saboda sun dira kan ‘yan ta’addan babu zato balle tsammani.

“Fiye da ‘yan ta’adda 15 aka halaka a take.”

- Majiyar tace saboda tana daga cikin sojojin da suka kai farmakin.

Yace:

“Dole ce ta sa ‘yan ta’addan suka janye da yawansu sakamakon raunikan da suka samu inda suka bar dabbobin da suka sace daga jama’a.”

Yace ‘yan ta’addan da suka tsere sun hanzarta kiran ‘yan uwansu yayin da zakakuran sojojin suka cigaba da bude wuta a duk hanyoyin da ‘yan ta’addan zasu iya shigowa.

Kara karanta wannan

Jiragen NAF Sun Yi Lugude Kan ‘Yan Boko Haram, Sun Aike Wasu Lahira

“Bayan kusan awa daya da rabi, ‘yan ta’addan sun karo mutanensu. Suna ta ihun Allahu Akbar amma dakarun suka cigaba da yi musu luguden wuta.
“Mun halaka karin bakwai daga ciki sakamakon musayar wutan da muka yi amma cike da takaici mun rasa dakaru biyu yayin da wasu jihar suka jikata yayin bin sauran ‘yan ta’addan da muka yi arangama.”

- Yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel