CBN Zai Dagargaza Naira Tiriliyan 6 Cikin Shekaru 8 a Mulkin Shugaba Buhari

CBN Zai Dagargaza Naira Tiriliyan 6 Cikin Shekaru 8 a Mulkin Shugaba Buhari

Bincike ya nuna Bankin CBN zai lalata takardun kudi na kimanin N6, 000, 000, 000, 000 a cikin shekaru kusan takwas

Babban bankin kasar yana bata duk kudin da suka tsufa ko suka yi rashin kyawun gani, sai a sake buga wasu sababbi

Kudin da aka kashe domin ayi waje da wadannan Tiriliyoyin kudi daga yawo a hannun jama’a sun kusa kai N4bn

FCT, Abuja - Ana sa ran babban bankin CBN na kasa zai lalata kudin da darajarsu ta haura Naira Tiriliyan shida a gwamnatin Muhammadu Buhari.

Binciken da Punch ta gudanar, ya nuna zuwa lokacin da Muhammadu Buhari, bankin CBN ya dagargaza takardun wadannan kudi da suka tsufa.

Bayanan da aka samu daga ofishin sashen ayyuka na babban bankin Najeriya ya nuna daga 2016 zuwa 2020, CBN ya dagargaza Naira Tiriliyan 4.1.

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN Ya Kawo Dalilin Goyon Bayan CBN Kan Buga Sabon Kudi

A tsawon shekarun nan biyar, an lalata wadannan takardun kudi da sun yi tsufa ko sun yi lalacewar da ba za a iya cigaba da amfani da su a Najeriya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar tace ba ta da bayanan adadin kudin da aka lalata tsakanin shekarar 2021 zuwa yanzu.

Amma bankin kasar ya bada sanarwar lalata 80% na Naira tiriliyan 3.2 da ke yawo. Wannan karo kudin za su tashi aiki ne saboda za a buga sababbi.

Gwamnan CBN
Gwamnan CBN Hoto: www.theunionnigeria.com
Asali: UGC

Tsakanin shekarar 2016 da 2020, alkaluman CBN sun nuna an lalata Naira biliyan 829.94 wadanda suka gurbace a dalilin kecewa ko makamancin haka.

A shekarar 2017 kuwa, Naira biliyan 977.23 aka lalata a babban bankin Najeriya na CBN.

A shekarun da suka biyo baya, adadin sun ragu; Naira biliyan 814.59 aka lalata a shekarar 2018, sai kuma aka dagargaza Naira biliyan 814.44bn a 2019.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Amince da Sauya Wasu Takardun Naira, CBN Tayi wa Ministan Martani

Jaridar tace a shekarar 2021 da ta biyo baya, takardar kudin Naira biliyan 698.59 aka lalata. Wannan ya sa aka bar jimillar adadin kan Naira Tiriliyan uku.

An kashe N3.88bn saboda a lalalta N3tr

Daga 2016 zuwa 2020, kudin da CBN ya kashe domin ya lalata wadannan kudi ya zarce Naira biliyan 3.8. Ana ware kudi masu yawo domin wannan aiki.

A 2016 an batar da N1.43bn, sai N594.6m, N662.2m, N647.8m da N538.5m a shekarun da suka biyo baya na 2017, 2018, 2019 da 2020 domin a lalata kudin.

Za a cire Ajami daga Naira?

A yau ne aka ji labari Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga Malaman addini su guji aiki da jita-jitar da ke yawo cewa za a cire Ajami daga takardun kudi.

Mai martaba kuma Khalifan Tijjaniya wanda ya rike bankin CBN yace ya tattauna da gwamnan babban banki kan wannan batu, an shaida masa rade-radi ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel