Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

  • Jami'an leken asirin Najeriya sun damke wasu mutum 35 da ake zargin yan ta'addan ISWAP ne a Abuja
  • Gwamnatin kasar Birtaniya ta saki sabon gargadi kan shirin kai hari Abuja kuma ta bada lambobin kira don agajin gaggawa
  • Hukumar kula da birnin taraya Abuja ta rusa gidaje, an rufe kantin Jabi Lake Mall da makarantu duk don tabbatar da tsaro

Hukumar tsaron farin kaya DSS, hukumar leken asirin Najeriya NIA, yan sanda da sauran jami'an tsaro sun kai harin kwantan bauna kauyukan Abuja kuma sun yi babban kamu.

Punch ta ruwaito cewa jami'an tsaron sun garkame kwamandojin ISWAP biyar da mayaka 30 a unguwanni irinsu Mararaba dake makwabtaka da ke kwaryar birnin tarayya Abuja.

Rahoton ya kara da cewa suna tsare yanzu a ofishin DSS.

Kara karanta wannan

Amurka Ta Shawarci Ma'aikatan Ofishinta Su Kwashe Iyalansu Daga Abuja Yanzu

Abuja
Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja Hoto: Abuja
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa hukumomin tsaron sun kwana biyu suna bibiyan yan ta'addan gabanin gargadin da Amurka da Birtaniya sukayi ranar Lahadi na cewa yan kasarsu suyi hattara da Abuja.

Wata majiyar tsaro da tayi karin haske kan lamarin tace yan ta'addan na shirin kai munanan hare-hare Abuja kafin aka kamasu.

Majiyar ta ce wadanda aka kama sun bada bayanai masu amfani wadanda suka taimaka wajen damke wasu mambobin ISWAP dake basaja da aikin ga ruwa, masu gadi, kanikanci, dss.

Wani babban jami'in tsaro da aka sakaye sunansa ya bayyana cewa:

"Ana gudanar da binciken kwa-kwaf domin kassara yan ta'addan ISWAP dake Abuja. An damke kwamandojinsu da yawa da yaransu kuma suna taimaka mana wajen bincike."
"An kama kimanin kwamandoji biyar da mayaka 30 kuma muna sa ran damke wasu yayinda muke cigaba da kokari."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

Yayinda aka tuntubi Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya bayyana cewa shi dai bai samu labarin haka ba har yanzu.

Shi kuwa Diraktan yada labaran hedkwatar tsaro, Manjo Jimmy Akpor, bai amsa kira ba.

Buhari Yayi Magana Akan Batutuwan Tsaro da Amurka, Burtaniya da Sauransu Ke Yi Kan Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bukaci 'yan Najeriya da su kwantar da hankala, amma su kasance a ankare kan shawarwarin tsaro da kasashen turai suka fara bayarwa kan birnin tarayya Abuja.

A cewar wata sanarwa da Buhari ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya shawarci 'yan kasa da jami'an tsaro da su zama masu sanya ido kan lamarin tsaron kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel