‘Yan Mata Sun Koka, Ana Yi Masu Aure da Tsofaffi Domin Iyayensu Su Biya Bashi

‘Yan Mata Sun Koka, Ana Yi Masu Aure da Tsofaffi Domin Iyayensu Su Biya Bashi

  • Wasu iyaye a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, su na aurar da yaransu da karfi-da yaji saboda talauci
  • Wata yarinya da tayi bayani tace ana yi masu aure da nufin iyayensu su samu kudin girbe amfanin gona
  • Yara sun kawo korafinsu ne a lokacin da aka yi bikin ‘ya ‘ya mata na Duniya domin a ji kukan diya mace

Abuja - Wasu sun koka da cewa ana aurar da yara masu kananan shekaru ga tsofaffi, abin takaicin shi ne iyaye na hada auren ne saboda abin Duniya.

Jaridar Guardian ta rahoto cewa an yi wannan korafi ne yayin da kungiyar Save the Children International (SCI) ta shirya taron ‘ya ‘ya mata a Abuja.

A makonnin da suka gabata aka yi murnar zagayowar ranar yara mata a Duniya. Najeriya na cikin kasashen da ake shirya bukukuwa na musamman.

Kara karanta wannan

Bana Bukatar Matar Aure Tunda Na Iya Girki Da Goge-goge: Matashi Dan Shekaru 47 Ya Ki Aure

Wata yarinya daga jihar Yobe, Khadija Badamasi ta shaida cewa a mahaifarta, ana yi wa yara mata aure saboda iyayensu su samu kudin da za suyi girbi.

Badamasi tace saboda mafi yawan mahaifansu manoma ne marasa karfi, su kan cin bashi ne domin su cire amfanin nomansu a gona da lokacin kaka.

Mata a gona
Wasu Mata a gona Hoto: www.betterlife-africa.org
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kukan da Khadija Badamasi tayi

“A lokacin girbi, idan uba bai da kudin da zai biya bashin da ya ci, yawanci mahaifi ya kan yanke shawarar aurar da diyarsa.
Uba zai yi hakan ne ba tare da duba shekarunta ba, mafi yawancin lokaci, sai ta auri wanda ya haife ta, ko ya yi sa’a da kakanta.
Ita kuwa amaryar ba ta da kima, ba a daukarta da daraja domin ganin yadda aka bada aurenta.”

Jaridar ta rahoto wannan Baiwar Allah ta cigaba da kokawa, tace ana yi wa ‘yan mata da-dama a kauyukansu auren dole, wanda hakan cin zarafin mace ne.

Kara karanta wannan

Musulmi da Kirista duk daya ne: Tinubu ya yiwa malaman addini jawabi a Kano

Muna cikin barazana - Madina Abdulkadir

Da take jawabi a taron da SCI ta shirya, This Day ta rahoto wata Madina Abdulkadir daga Dikwa a Borno, tayi magana a kan muhimmancin ilmintar da mace.

Madina tace mata su na fuskantar barazana wajen samun ilmi da sauran bukatu na yau da kullum a fadin Duniya, wanda ya kamata a kawo karshen wannan.

Tasirin canza kudi

Kamar yadda Janar Muhammadu Buhari yayi a lokacin mulkin soji a 1984, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele yace za a fito da sababbin kudi.

Mun kawo rahoton yadda tattalin arziki zai motsa a sanadiyyar wannan mataki ta fuskar karyewar Naira a kan Dala da tashin farashin kaya a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel