Ka Taimaka Ka Aureni ta 10, Kyakyawar Budurwa Ta Roki Ooni na Ife

Ka Taimaka Ka Aureni ta 10, Kyakyawar Budurwa Ta Roki Ooni na Ife

  • Wata mata wacce bata bayyana sunanta ba ta dinga rokon basarake Ooni na Ife, Oba Adeyeye da ya aureta matsayin mata ta 10
  • Ta sanar da cewa ta san ya tsara matan da zai aura amma ya taimaka ya aureta matsayin ta 10 kuma ita Ibo ce daga Abia
  • Ta sanar da cewa zata rungumi ‘ya’yansa hannu bibbiyu kuma zata kwantar masa da hankali matukar ya aureta matsayin mace ta 10

Wata mata ‘yar kabilar Ibo ta roki Ooni na Ife, Oba Adeyeye Oguwusi da ya aureta matsayin mata ta goma.

Matar a wani bidiyo da ta bayyana, tace ita ‘yar asalin jihar Abia ce kuma ta roki Ooni na Ife da ya aureta, Daily Trust ta rahoto hakan.

Igbo Woman
Ka Taimaka Ka Aureni ta 10, Kyakyawar Budurwa Ta Roki Ooni na Ife. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ooni ya shiga kanun labarai a cikin kwanakin nan bayan ya auri mata biyar a cikin wata biyu kacal.

Kara karanta wannan

A Raba Ni Da Matata Kafin Hawan Jini Yayi Ajalina, Magidanci ga Alkali

Akwai labarai da ake bayyana kan basaraken da aurensa ya dinga rabuwa cewa bai gama ba. Yanzu kuwa mata a bidiyon bata bayyana sunanta ba amma tace ta shirya auren basaraken.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tace ta yuwu basaraken ya shirya matan da zai aura tuni, don haka ba zata damu ba idan ya aureta matsayin mata ta goma.

Tace:

“Gareka ran ka shi dade, a madadin mutane na, ina son neman gurbin zama daya daga cikin matan ka saboda dole akwai wani abu da suka hango a tattare da kai.
“Ina son zama matar ka ta 10 saboda na san yanzu kana da wadanda kake so ka aura, baka zo karamar hukumata ba amma muna nan muna jiran ka.
“Ranka shi dade ina da girma, fara ce kuma ina da karamin kasuwanci da nake yi. Ina rokon ka.

Kara karanta wannan

Venza zan siya: Budurwa ta yi asusu tun 2021, ta tara kudade masu ban mamaki

“Ka taimake ni daga Abia nake, ina son saka fararen kaya nima. Ina son fararen kaya, ina da tsayI, ka taimake ni.”

Matar ta sha alwashin bai wa ‘ya’yan shi kula ta musamman idan ya aureta kuma ba zata dinga tada masa hankali ba.

Bayan Auren Mata ta 3 a Makon da Ya Gabata, Ooni na Ife ya Auro Mata ta 4 a Makon nan

A wani labari na daban, Ooni na Ile-Ife, Oba Enitan Oginwusi, Ojaja II ya auro sabuwar mata mai suna Ashley Adegoke inda ya shiga da ita fadarsa a cikin wani kasaitaccen biki.

Auren na zuwa ne bayan makonni da basaraken ya yi wani auren inda ya aura Mariam Anako a wani takaitaccen bikin.

An tattaro cewa, basaraken ya auri Adegoke a ranar Juma’a da ta gabata. Hakazalika an yi auren ne a gidansu amaryar dake titin Olubose kan titin Ede a Ile-Ife.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng