A raba ni da matata kafin in halaka ta - Magidanci ya sanar da kotu

A raba ni da matata kafin in halaka ta - Magidanci ya sanar da kotu

Wani tsohon direban tasi mai suna Ganiyu Adenekan, ya bukaci wata kotun gargajiya da ke zama a Ake, Abeukuta da ke jihar Ogun a kan ta tsinke igiyar aurensu mai shekaru 22 da matarsa mai suna Morufat. Kamar yadda yayi ikirari, zai iya kashe ta.

Adenekan ya sanar da kotun cewa aurensu ya kai shekaru 10 cikin rashin kwanciyar hankali da banbance-banbance wadanda aka kasa shawo kansu. Ya ce Morufat na son halaka shi don haka a tsinke igiyar aurensu tun kafin yayi nasara a kanta.

Mai karar dai ya kara da bukatar kotun da ta bashi rikon yaransu uku masu suna Toheeb, Rasak da Abiodun, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, "Dukkan dangin mu sun gaji da matsalarmu. Kusan shekaru 10 kenan muke maneji amma lokaci yayi da zamu rabu. Bana son ta kashe ni. Idan da zan bude jikina yanzu, da kun ga tabbai da tayi min. Bata yi nasarar kashe ni ba amma zan iya nasara a kanta. Tun kafin in yi kisan kai, gara a rabamu."

A rabani da matata kafin in yi nasarar halakata - Magidanci ya sanar da kotu
A rabani da matata kafin in yi nasarar halakata - Magidanci ya sanar da kotu
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Batan N36.8m a hukumar JAMB: An gano 'macizan' da suka wawure kudin

Morufat wacce bata ki a raba auren ba, ta zargi Adenekan da rashin daukar dawainiyar da ta hau kansa. Tace duk zargin da yayi mata kawai bacin suna ne. Ta bukaci kotun da kada ta bashi rikon yaransu don ba zai iya basu tarbiya mai kyau ba.

Alkalin kotun, A. O Abimbola ta tambaya Rasak da Abiodun a kan wanda za su so zama dashi amma sai suka ce mahaifiyarsu.

A lokacin da alkalin ta so jin nawa Adenekan zai iya biya na kula da yaran, sai yace "Mai shari'a, a wannan shekarun nawa, ya zan iya bada kudin ciyarwa bayan yaran da za su dinga min aike-aike suna wajenta? Idan kotu ta amince ta karbe yaran, toh a sanar mata ta shirya kula dasu."

Alkalin kotun ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 27 ga watan Afirilun 2020 don yanke hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: