Jiragen NAF Sun Yi Lugude Kan Attajirin ‘Dan Ta’adda Sububu da Mukarrabansa, 30 Sun Mutu

Jiragen NAF Sun Yi Lugude Kan Attajirin ‘Dan Ta’adda Sububu da Mukarrabansa, 30 Sun Mutu

  • Luguden da jiragen yakin NAF suka yi kan Halilu Sububu da kungiyarsa yayin da suke muhimmin taro a inda yake adana kayayyakinsa yayi ajalin ‘yan ta’adda 30 a Zamfara
  • Dakarun sun gano cewa Sububu da mukarabbansa sun shirya taron sassafe wanda hakan yasa suka yi dirar mikiya a kansu da safiyar 21 ga watan Oktoban 2022
  • Majiya ta tabbatar da cewa Halilu shi ne attajirin ‘dan ta’addan dake safarar makamai tare da rarrabawa ‘yan ta’adda a yankunan jihar Zamfara

Zamfara - A kalla ‘yan ta’adda 30 ragargazar dakarun sojin saman Najeriya ta jiragen yaki yayi ajali yayin wani samame da suka kai maboyarsu a jihar Zamfara, jaridar Punch ta rahoto hakan.

Jirgin Yakin Soji
Jiragen NAF Sun Yi Lugude Kan Attajirin ‘Dan Ta’adda Sububu da Mukarrabansa, 30 Sun Mutu. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Wata majiya daga rundunar sojin ta sanarwa Punch cewa Halilu babban ‘dan ta’adda ne da ya kware wurin safarar makamai ga sauran ‘yan ta’addan da suka addabi jihohin Zamfara da Katsina.

Kara karanta wannan

Dandazon Yan Ta'adda Sun Sheka Lahira Yayin da Jirgin Soji Ya Musu Ruwan Bama-Bamai a Jihar Arewa

Majiyar ta bayyana cewa:

“Halilu shi ne Attajirin ‘dan ta’adda dake tafka tsiya da suka hada da garkuwa da mutane, satar shanu da sauran ayyukan ta’addanci.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An san cewa yana yawan zuwa Sububu, Bayan Daji a Anka da yankin Bayan Ruwa a Zamfara.

Halaka ‘yan kungiyar Halilu ya biyo bayan gamsassun bayanan sirri ne wadanda suka bayyana cewa Halilu ya tsara wani taron sassafe da sauran sojojinsa a inda yake ajiyar kayan aiki a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

“Bayan kwanaki da makonni na tattaro bayanan sirri kan abinda zasu da inda zasu yi, jiragen Yakub NAF a sa’o’in farko na ranar 21 ga watan Oktoban 2022 sun tsinkayi wurin taron da ajiye kayan aikin.
“Duba inda abun ya faru Bayan luguden wutan da aka yi musu ya bayyana cewa an tarwatsa wurin taron da ma’adanar kayayyakinsa. Bayani daga mazauna yankin ya tabbatar da cewa an halaka ‘yan ta’adda masu tarin yawa a wurin taron duk da babu tabbacin ko Halilu ya sheka lahira.”

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 27 Daga Masu Garkuwa da Mutane

Zamfara: An Damke Masu Samarwa ‘Yan Bindiga Layikan Waya da Maganin Karfin Maza

A wani labari na daban, kwamitin yaki da dabanci na gwamnatin jihar Zamfara sun tabbatar da kama wasu mutum uku da ake zargi da samarwa ‘yan bindiga layikan waya, kwayoyi da maganin karfin maza.

TheCable ta rahoto cewa, kwamitin ya kama wasu mutum uku kan zargin kwacen waya.

Bello Bakyasuwa, shugaban kwamitin yayi maganar a ranar Lahadi yayin mika wadanda ake zargi hannun jami’an tsaro a Gusau, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel