Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 27 Daga Masu Garkuwa da Mutane

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 27 Daga Masu Garkuwa da Mutane

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar da ceto wasu mutum 27 daga hannun masu garkuwa da mutane a dajikan Gando/Bagega da Sunke
  • A halin yanzu, mutum 17 daga cikin wadanda aka ceto suna hannun ‘yan sanda yayin da 10 daga ciki suke asibiti domin samun taimakon likitoci
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Kolo Yusuf, ya bayyana cewa kiran gaggawa suka samu daga kauyukan Akawa, Gwashi, Tungar Rogo da Anka na satar jama’a

Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ceto mutum 27 da aka yi garkuwa dasu a kauyukan Akawa, Gwashi, Tungar Rogo da Anka wadanda ‘yan bindiga suka kai sansanoninsu na Gando/Bagega da dajikan Sunke a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka a jihar.

Kara karanta wannan

Borno: Sojojin Najeriya Sun Halaka ‘Yan Ta’adda 31, Sun Damke 70 a Borno

Jihar Zamfara
Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 27 Daga Masu Garkuwa da Mutane. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa, a yayin jawabi ga manema labarai a ranar Asabar, kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Mohammed Shehu, yace cetonsu ya biyo bayan rahoton da Rundunar ta samu ne kan cewa kungiyar ‘yan ta’addan sun kutsa wasu kauyuka a Anka da Bukkuyum inda suka sace mutane da ba a san yawansu ba.

Yace:

“Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sanda Kolo Yusuf ya aike karin ‘yan sanda domin su taimakawa na Anka da Bukkuyum tare da ‘yan sa kai wurin ceto wadanda aka sace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Cike da sa’a, an yi bincike mai kyau kuma an ceto su da taimakon shugabannin kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.”

Yayi bayanin cewa, 17 daga cikin 27 da aka ceto an kai su hedkwatar ‘yan sanda yayin da sauran 10 aka mika su asibiti inda suke samun taimakon likitoci sakamakon firgicin da suka shiga, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji Sun Ragargaza Fitaccen Shugaban ‘Yan Bindiga Zamfara, Chire

Shehu yace dukkan wadanda aka ceto an yi musu jawabi kuma za a mika su hannun kwamishinan tsaron cikin gida wanda a madadin Gwamna Bello Matawalle zai mika su ga iyalansu.

Kwamishinan ya yabawa Gwamna Matawalle kan goyon bayan da kwarin guiwa da ya bai wa ‘yan sanda da hukumomin tsaro a kokarinsu na ganin bayan ‘yan ta’adda a jihar.

Kwamishinan ya kara da taya wadanda aka ceto murnar samun ‘yanci tare da tabbatarwa da jama’a cewa ba zasu sassauta ba wurin ganin bayan ‘yan ta’adda tare da saka su su fuskanci shari’a.

Zamfara: ‘Yan Daba Sun Lakadawa Shugaban ‘Yan Jarida Mugun Duka, Sun yi Barazana ga Jami’ai

A wani labari na daban, Wasu da ake zargin ‘yan daba ne a ranar Alhamis sun lakadawa shugaban ‘yan jaridan jihar Zamfara, Kwamared Ibrahim Maizare mugun duka tare da yin barazanar cin zarafin duk manema labaran dake aiki a jihar.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Bindige Masu Garkuwa da Mutane 2, Sun Samo Kudin Fansa N8.4m a Bauchi

‘Yan daban sun fada shugaban ‘yan jaridan da suka ne bayan ya bukaci wasu ma’aikata dake gyaran wani shago a sakateriyar ‘yan jaridan da za a yi amfani da shi don kamfen da su tsaya da aikinsu, Channels TV ta rahoto hakan.

‘Yan daban sun ce ba zasu daina aikin ba ko kuma su bar wurin saboda ‘dan siyasa ne ya basu wurin kuma matukar yana numfashi ba zasu bar wurin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel